Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Tayi Kashedi Akan Cibok


Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki Moon.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki Moon.

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa idan 'yan bindiga suka sayar da dalibai mata, kamar yadda wanda yake cewa shine shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yayi barazana, to zata neme su, bisa tuhumarsu da laifukan yaki, ko anyi shekaru masu yawa sosai bayan aukuwar lamarin.

"Muna gargadin masu gudanar da laifi, da cewa an haramta aikin bauta da kuma bautar fasikanci a karkashin dokar kasa da kasa. Zai iya kasancewa laifin keta hakkin bil adama," a cewar kakakin kwamitin 'yancin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Rupert Colville a birnin Geneva.

Gazawar sojojin Najeriya wajen ceto daliban a cikin makonni ya jawo zanga-zanga a duk fadin duniya, da kuma birane a Najeriya kamar Abuja, da Ikko birnin kasuwanci. Ana kyautata zaton za'a cigaba da zanga-zanga a Abuja a dai-dai lokacin da Taron Tattalin Arzikin Duniya yake wakana.

An jibge tarin 'yan sanda da sojoji a gaban Otel din Sheraton dake saukar baki a Abuja, kana akwai wata bakar mota dauke da mutane hudu sanye da bakaken kaya dauke da bindigogi tana safara.

Daliban da aka sace masu rubuta jarrabawarsu ta karshe a Makarantar Sakandaren Cibok dake Jihar Borno, su kai 270 da wani abu, kuma sun kunshi dalibai mata daga wasu makarantun Sakandaren wadanda suke makarantar musamman domin daukar jarrabawar.

Jami'an Najeriya a baya sunyi ikirarin ceto kusan duka daliban, inda ma suka ce 8 ne kawai suka rage, daga baya kuma kakakinta Manjo Janar Chris Olukolade wanda ya bada sanarwar farko, ya janye wadannan kalamai na zuki. Ministan Yada Labarai Labaran Maku shima a kwanakin baya yace jami'an tsaro suka kan hanyarsu na kwato daliban, amma Lahadinnan da Shugaba Jonathan yake ganawa da manema labarai, Mr. Jonathan ya nuna cewa bashi da cikakkiyar masaniya game da batun Cibok.

Yanzu dai an fara nuna hannu akan ko wanene ya kwashe daliban. Majalisar dokokin Jihar Borno na nuna Shugaba Jonathan, ita kuma uwar gidan Shugaba Jonathan na dore alhakin sace daliban akan Gwamna Kashim Shettima. Ana tsakiyar wannan ne kuma mutumin da yake cewa shine shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani bidiyo da yake cewa sune suka sace daliban, makonni uku da sace su. A daren jiya kuma an kara sace wasu yara mata masu shekaru daga 12 zuwa 15 a karamar hukumar Gwoza dake Jihar Borno.

Hankulan jama'a sun koma kan yadda Shugaba Jonathan yake takalar yaki da ta'addanci, musamman ma tun bayan gangamin siyasa da ya hallarta a Kano, inda yayi rawa kwana daya bayan sace daliban mata sama da 200, da fashewar Bom na farko a Nyanya, Abuja, lamarin da yayi sanadiyar rayuka a kalla 75 da jikkata sama da dari. Yanzu jama'a a manyan birane a duk fadin duniya kamar New York, da London, da Washington D.C na zanga-zangar lumana, suna kira ga gwamanti akan ta tabbatar an samo wadannan daliban mata masu rubuta jarrabawar karshe.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG