Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan Ya Sace Daliban Cibok – inji Majalisar Borno


A dai-dai lokacin da aka share makonni uku da sace dalibai mata sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok, Majalisar Dokokin Jihar Borno ta dorawa Shugaba Goodluck Jonathan alhakin sace yaran.

Majalisar Dokokin Jihar Borno, ta bakin dan majalisa kuma shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Honorable Muhammad Sale Banga na zargin shugaba Jonathan da sace dalibannan mata wadanda aka sace a makarantarsu ta sakandare dake Cibok.

“Mu a Jihar Borno, da kuma Yobe, bazan tsaya a Borno kadai ba, ka ga wannan abu ya faru a FGC Buni Yadi a Jihar Yobe, sannan kuma aka debe wadannan daliban sama da dari biyu, to ana kan wannan ce-ce ku-ce, sai ga magana daga fadar shugaban kasa, tunda matar shugaban kasa ce, take cewa a gayawa Gwamnan Borno, Ya fito da wadannan ‘yan matan. To idan ba’a manta ba, akwai lokacin da gwamnan Bornon ya fito yake cewa mutanennan, wadannan ‘yan kungiyar suna da makamai fiye da jami’an tsaron kasa. Aka yi masa ca, a wannan lokacin,” a cewar Hon. Banga. “Hatta shi shugaban kasa, abunda ya furta yace da zai janye sojojinsa, gwamnan Borno bai isa ya shiga ofishinsa ba, bai isa ya shiga gidan gwamnati ba.”

Hon. Muhammad Sale Banga ya cigaba da cewa “yau bamu sani ba, janye sojojinnan yayi ne, sannan aka zo aka kwashe ‘yan matannan a makarantarnnan na Cibok? ko kuma a’a akwai jami’an tsaron da shugaban kasa ya baiwa Gwamnan na Borno, sannan shi kuma ya basu umarnin kwashe wadannan dalibai, sannan har tace shi Gwamnan Bornon ya dawo da daliban?”.

“Ai wannan magana, ana cewa idan mai magana wawa ne, maji magana ba wawa bane,” a cewar Hon. Banga. “Gaskiyar magana, ta (Matar shugaban kasa) tambayi fadar shugaban kasa, ta tambayi mijinta sannan ya saka jami’an tsaro, a matsayinsa na shine shugaban jami’an tsaron Najeriya baki daya, wato nan da ‘yan kwanaki kadan, ba tare da bata lokaci ba da gaggawa, yadda asiri yake tonuwa, asiri ya tonu, su fito da wadannan ‘yan matan.”

Yanzu dai misalin makonni uku kennan da sace daliban su sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe.

Shugaba Jonathan lahadinnan yayi alkwarin ceto daliban a ganawar da yayi manema labarai.

A halin yanzu dai jama’a sun share kwanaki 6 suna gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Abuja domin kira ga hukumomi su mayar da hankali wajen ceto wadannan yara.

Yanzu dai an tsare shugabar matan Cibok dake wannan zanga-zanga bayan ganawa da tayi da matar shugaban kasa a birnin na Abuja.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG