Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadai da Lamarin Cibok – inji Senatocin Amurka


Shugaban Amurka Barack Obama da Senata Barbara Boxer da sauran jami'an gwamnati.
Shugaban Amurka Barack Obama da Senata Barbara Boxer da sauran jami'an gwamnati.

Wasu daga cikin Senatocin Amurka sun gabatar da kuduri a gaban Majalisa mai Allah wadai da sace dalibai mata na Makarantar Sakandare dake Cibok, Jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Senata Barbara Boxer ‘yar jam’iyyar Demokrat daga Califoniya, da Mary Landrieu ‘yar Demokrat daga Luwisiyana, da Jim Inhofe Republican daga Oklahoma, da Dick Durbin Demokrat daga Illinois, da Chris Coons Demokrat daga Delawaya, da ma Robert Menendez shima Demokrat daga New Jersey Alhamis dinnan suka gabatar da wani kuduri mai Allah wadai da satar dalibai da aka yi ran 14 ga watan Afrilu, inda aka yi awon gaba da mata su a kalla 234. Jami’ai sunce wasu daga cikin dalibai sun kubuce, amma kusa 200 da wani abu yanzu haka suna hannun ‘yan bindiga, yaranda shekarunsu suka kama daga 16 zuwa 18. Rahotanni dake zuwa daga yankin na nuna kamar ana sayar da yaranne ta yi musu aure da sadakin $12, wato Naira dubu 2.

“Kaiwa yara mata hari, da sace su kawai saboda suna zuwa makaranta abun takaici ni, kuma baza a taba yin shiru ba,” Senata Boxer tace. “Kungiyoyin kasa da kasa ya kamata su nuna a fili cewa duk yara na bukatar daman neman ilimi ba tare da an razana su ba, kuma masu yin duk irin wannan ta’asa, za’a hukunta su.” Senata Boxer itace take jagorancin Kwamitin Majalisar Dattawa mai lura da ayyukan kasashen ketare, da ‘yancin bil adama, Demokradiyya da harkokin mata a duk fadin duniya.

“Ina mai matukar damuwa da satar dalibai mata su 234, wadanda yanzu haka 191 ba’a gansu ba, a arewa maso gabashin Najeriya. Wannan ya nuna irin kalubalen da mata ke fuskanta a duk fadin duniya wajen samun ‘yancin kansu da matan Amurkawa ke morewa. Wannan kuduri na Senatoci ya nuna goyon bayan Majalisar Dattawan Amurka ga jama’ar Najeriya, musamman iyaye da iyalan wadannan dalibai, da sauran jama’a wadanda tashe-tashen hankulan ‘yan bindiga suka shafa, da kuma yin Allah wadai da munanan hare-hare akan fararen hula,” a cewar Senata Landrieu. “Wannan kudu ma ya mayar da hankali akan baiwa mata karfin gwiwar cewa suna daga cikin gimshiken cigaba da tsaro da demokradiyya a al-ummominsu idan suna da ilimi. Idan maza da mata suna samun daman neman ilimi dai-dai, ana samun bunkasar tattalin arziki, iyalai na kara karfi sannan al-umma na cigaba.”

Yanzu an shekare sama da makonni da sace dalibai mata su sama da 200, wadanda ‘yan bindiga suka abkawa cikin dare, suka kona makarantarsu kana suka kwashe su a cikin manyan motoci suka tafi dasu.

Daliban na rubuta jarrabawar karshe ta fita daga makarantar Sekandare ne, yawancinsu ‘ya’yan masu karamin karfi ‘yan bindiga suka tafi dasu, amma wasu sun daga cikinsu sun gudu har suka bada labarin yadda ‘yan bindigan dake tsare dasu suke shirin tafiya wani wajen dasu.

Hukumomin Najeriya, musamman Ma’aikatar Tsaron Kasa ta fitar da sanar ta bakin kakakinta Manjo Janar Chris Olukolade, na cewa ta ceto duka daliban, kalaman da jami’an makarantarsu da iyayensu suka karyata, kuma hukumar tsaron ta janye kalamunta daga baya.

Ya zuwa yanzu babu ya tabbatar da inda wadannan yara suke, amma a kwanakin baya dan Majalisar Wakilai a Tarayya, daga Jihar Borno Alhaji Muhammad Tahir Monguno ya gayawa Muryar Amurka cewa ya samu labarin cewa ‘yan bindigan na daurawa junansu aure da yaran.

Kungiyoyin mata da iyaye da dalibai a Najeriya da wasu kasashen ketare sun gudanar da zanga-zanga domin kira ga gwamnati ta dauki matakin kwato daliban.

Ya zuwa yanzu, jami'ai basu sanar da iyayen daliban ko me ake ciki ba, game da aikin neman yaransu.

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG