Amma taron ya kasance tamkar taron yiwa daliban da wasu 'yan bindiga suka sace ne addu'a ta musamman ganin tsawon lokacin da malamai suka kwashe suna addu'a. An gudanar da addu'o'in ne domin samun mafita ga daliban da aka sace a garin Chibok na jihar Borno. Haka kuma malaman sun yi addu'ar samun masalahar Ubangiji ga jama'a da jihohin dake fama da hare-hare a arewacin kasar.
Zaben shugabannin APC a jihar Sokoto ya kasance ta hanyar sasantawa ne inda Bala Abubakar ya zama sabon shugaban jam'iyyar na jihar. Duk da sukar da jama'a keyi na hana yin zaben fitar da shugabanni, gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamako na ganin itace hanya mafi sauki a kokarin magance rarrabuwar kawuna.
A jihar Zamfara ma bata sake zani ba. Shugaban rikon kwarya Lawali Makaman Kaura jam'iyyar tace shi ya zama tabbatacen shugaban jam'iyyar na jihar lamarin da ya sa wasu suna korafin an hanasu tsayawa takara karfi da yaji kamar irinsu Mohammed Dole. Yace ya je har Abuja ofishin jam'iyyar inda ya biya kudi ya yanki takardar shiga takara amma abun mamaki sai jam'iyyar ta gabatarda Lawali a matsayin shugaban jihar.
Ga karin bayani.