Mr. Shettima ya soma ne da nuna juyayinsa ga iyayen wadannan yara, da kuma yi musu alkawarin cigaba da neman inda wadannan yara suke.
A lokacin da yake wa iyayen yaran jawabi, yana share hawaye daga idanunsa, yace “abunda ya same mu dinnan, ya shafi duk mutumin kasarnan. Ya shafi duk mutumin duniya. Yara ne basu san hawa ba, basu san sauka ba, sunzo neman ilimi, tsirarun yara suzo su debe su. Jami’an tsaro suna gwargwadon karfinsu, a yanzu haka ma suna gwagwarmayar kwato ‘ya’yanmu. Amma bai can-canta in bada bayani fiye da haka ba. InshaAllah, inshaAllah, inshaAllah za’a samu yarannan a cikin koshin lafiya. Dole mu baku hakuri, wannan masifa ce ta fado a kanmu, kuma in Allah Ya yarda, Allah Zai ceto mu.”
Shima dan majalisa mai wakiltar mazabar kudancin Borno Senata Muhammad Ali Ndume yayi wa iyayen jawabi cikin jimami da tausayawa kamar haka.
Senata Nduma yace “dalilin da muka zo nan, shine don ku sani, muna tare da ku, abunda ya same ku, ya same mu. Meye shugaba idan jama’arsa suna cikin kunci? Babu amfani! Mene ne shugaba idan kai kana da lafiya, wadanda kake shugabanci basu da zaman lafiya? Allah Ya jarrabce mu da wannan shugabanci a lokacin da mu dinma, babu abunda zamu iya yi, sai dai muyi jagora mu koma ga Allah mu roki Allah Ya kawo mana saukin wannan abun.