Matakan wadanda ba'a bayyana gundarinsu ba, sun kunshi bunkasa hanyoyin tattaro bayanai, da hada kan sojoji, da kuma hukunta masu laifi idan aka kama su.
Fadar da Shugaban kasa ta bayyana lamarin Cibok a matsayin "tashin hankali", da kuma "al-fasha". Kakakin yace sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yana kan hanyarshi ta zuwa Najeriyan domin tattauna wannan batun da masu wasu batutuwan.
Yanzu an share kusan mako daya kennan ana zanga-zangar lumana a sassa daban-daban a duniya, dake kiran hukumomin Najeriya su dauki matakan neman wadannan yara sama da 200 da aka sace.
A kwanakin baya, hukumar tsaron Najeriya ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye suka karyata, sai kuma daga baya hukumar ta janye kalamanta.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a ganawar da yayi da manema labarai Lahadinnan, yayi alkawari samo wadannan yara, wanda yace yanzu haka ba'a tabbatar da inda suke ba, da kuma adadinsu.