Da ya ke bayani ma abokin aikinmu Bello Habib Galadanchi, daya daga cikin iyayen 'yan matan ya ce a baya-bayan nan sun ji cewa an ga 'yan matan a wajejen Monguno da Marte da Kukawa da dai sauransu. Ya ce a baya an gaya masu cewa 'yan matan na dajin Sambisa har wasu iyayen su ka je wurin sai kuma gashi su na jin jita-jita iri-iri. Ya ce har yanzu iyaye dai na kai kukansu wurin gwamnati. Kuma akwai wajen 'yan mata 193 a hannun 'yan bindigar.
Ya ce kwanan baya an gaya masu cewa 'yan bindigar na shirin wucewa da 'yan matan zuwa wani wuri a jihar Adamawa don haka su ka fito da matasan garin su ka tare hanya amma ba su ga kowa ba. Ya ce gashi yanzu kuma ana ce masu ana jin duriyar 'yan matan a wajejen Monguno da Marte da sauransu. Ya ce wannan al'amari ya jefa su cikin matsanaciyar damuwa.