Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Shugabar Matan Cibok a Abuja


Cibok Protests 'Bring Back Our Girls', May 3, 2014
Cibok Protests 'Bring Back Our Girls', May 3, 2014

​Biyo bayan ganawar da tayi da matar Shugaban Kasa Mrs. Patience Jonathan, hukumar ‘yan sandan farin kaya wato SSS ta tsare shugabar matan Cibok a birnin Abuja, Naomi Nyadar.

‘Yan Sandan farin kaya a Najeriya, wato SSS sun tsare Naomi Mutah Nyadar, shugabar matan Cibok a birnin Abuja, kuma daya daga cikin shugabannin masu zanga-zangar lumana a birnin na Abuja, masu kira akan gwamnati ta kara kaimi wajen gani an kubutar da daliban Cibok da aka sace su sama da dari biyu, misalin makonni uku kennan.

Wannan tsare Mr. Naomi Nyadar da aka yi, ya biyo bayan ganawar da tayi da maid akin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa.

Ya zuwa yanzu hukumomi basu ce komai game da kama Mr. Nyadar ba.

Litinin dinnan, kwanaki 6 kennan ana zanga-zangar lumana a birnin Tarayya Abuja, inda jama’a suke neman gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen ceto dalibai mata da aka sace a lokacin da suke rubuta jarrabawarsu ta karshe.

A kwanakin baya, hukumomin Najeriya sunce sun kubutar da kusan duka daliban, ta bakin kakakinta Chris Olukolade, amma daga baya ta janye kalamanta.

Labarai masu alaka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG