Wani mahaifi cewa yayi “mun damu, mu iyayen yara, tun ranar Litinin, bamu ga inda aka shiga da ‘ya’yanmu ba. Sai muka dauka “machine” guda 150 muka shiga cikin daji muka je muka tarar da gidaje. Mun tarar da mutum, ‘yan mata da mata sun kai sama da goma sha wani abu, muna tafiya, muna tafiya, munyi tafiyar kilomita 25, bamu ga rana ba, sai muka je muka samu wani gadan da aka yi da itace, sai muka shiga karkashin gadan. Sai aka tsayar da mu, aka ce mana jejin nan, babu gari. Wasu “machine” sun lalace, ya kai shekaru 4, machine baya tafiya a “area” din. Sai wasu suka zo, muka ce musu kun san labari? Sai yace kwarai, kamar misali karfe tara, ‘ya’yanku sunzo sun tsaya a nan. Ya kai minti goma sha biyar. Amma kunga wannan hanyar, sune suka sauka. Wadancan itace, idan kuka wuce wadancan itace, baza ku fita da rai ba. Da ku da ‘ya’yanku, duka za’a gama da ku. Wadannan wurin mun gani, babu iyakar abu, idan zamu kirga abubuwan da muka gani da idanunmu a cikin dajin, abun zai kawo kuka ne.”
Wani mahaifin daya daga cikin yaran mata shima ya bayanna nasa zuciyar “ni daya daga cikin wadanda ‘ya’yansu aka dauke ne. Bayani, abunda yake akwai daki daki, bayan wannan abu ya faru, kowa ya zo makarantarnan, kuma da muka bincika, yaranmu guda 234 babu, shine zahirin magana. Wadanda aka samu kuma, guda 39, ko ba haka ba jama’a?”
Jama’a suka ce “haka ne”.
Shine mutumin ya cigaba da cewa “mai girma gwamna, mun gode maka, kada kayi gajiya, lokacin da wannan abu ya faru, ba’a bi sawunsu bane, kamar yadda na baya fada, mu iyaye mune muka fita. Ka kawo mana jami’an tsaro su bi sawun yarannan namu a same su.”
Iyayen dai sun cigaba da kira ga gwamnati da hukumomi akan su taimaka a bi sawun inda yaran suke, domin sako su da lafiyarsu.