Hukumar tsaron Najeriya a baya ta fitar da sanarwar ceto kusan duka ‘yan matan, kuma daga baya ta janye kalaman nata.
Shi kuwa gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayi alkawarin bada naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka ceto matan.
Ya zuwa yanzu dai hukumomi basu fitar da wani bayani ba game da inda aka kwana, a yunkurin ceto yaran wadanda yawancinsu matasa ne.
Daya daga cikin iyayen ya nuna damuwarshi matuka akan yadda hukumomi suka gaza wajen sanar dasu inda aka kwana.
“Batun yarannan an barmu a cikin duhu, babu abunda akayi. Ba’a yi mana komai ba”, a cewar daya daga iyayen.
Mutumin ya kara da cewa “yanzu abinda iyaye suke shirin yi “demonstrations” ne”.
Ya zuwa yanzu dai ba’a bayyana lokacin da za’a yi wannan zanga-zanga ba, amma an shirya za’a yi shine a karamar hukumar ta Cibok dake jihar Borno.
Yanzu haka sama da makonni biyu kennan da sace yara mata dalibai su sama da 200 daga makarantar Sakandarin Gwamnati dake Cibok a jihar Borno, a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe ta fita daga makaranta.