Mr. Bakari yace “mun dage akan cewa kazafin dake zuwa daga Najeriya, mai cewa wasu daga cikin dalibai mata su 200 wadanda aka sace a baya-bayannan an yi musu auren dole a Kamaru da ‘ya’yan Boko Haram, wannan kalami bashi da tushe. Kamaru baza ta taba zama tugar masu tayar da zaune tsaye ba ga wasu kasashen.”
Bakari yace wannan ba shine karo na farko ba da aka saka Kamaru a cikin lamarin da ya kira laifuka na “cin zarafi da marasa dadi” dake wakana a Najeriya. Amma ya maimaita cewa kasarshi a tsaye take wajen yakar ta’addanci tare da hadin kan jami’an Najeriya sauran kawayenta na yankin.
Ya zuwa yanzu hukumomin Najeriya basu da tabbacin inda wadannan dalibai suke, inda ma Shugaba Jonathan Lahadinnan yace bai san adadin yaran da aka kwashe ba. Sai dai kuma a kwanakin baya, hukumar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwa ta bakin kakakinta, Chris Olukolade wanda yace an kubuto da duka daliban, kalaman da iyaye suka karyata, kuma daga baya Manjo Janar Olukolade ya janye kalamunsa.
Yanzu dai maza da mata a sassa daban-daban na duniya na gudanar da zanga-zangar lumana domin kira ga hukumomin Najeriya akan su hanzarta wajen ceto wadannan yara mata da aka sace.