'Yan kungiyar daliban sun yi kira ne bayan taron da suka yi a Maiduguri inda suka nuna takaicinsu da sace daliban da yanzu kungiyar Boko Haram ta tabbatar cewa ita ce ta sacesu. Daliban sun ba gwamnati kwanaki arba'in gwamnati ta kubuto da yaran idan kuma ta kasa zasu kira taron kasa a Maiduguri domin nuna rashin gamsuwarsu.
Ahmed Shehu shi ne shugaban kungiyar jakadun wanzar da zaman lafiya dake wakiltan matasan dake fafitikan wanzar da zaman lafiya a arewa maso gabashin Najeriya. Yana cikin wadanda suka halarci taron. Yace su matasa da daliban su ne abun ya fi shafa domin wadanda aka sace yara ne dalibai. Yace idan basu yi wani abu ba to gobe lamarin ka iya faruwa da su. Yace dole rawar ta canza idan za'a gano daliban. Daliban suna bukatar a kauracewa azuzuwa a duk fadin duniya.
Malamai ma sun goyi bayan matakin da gamayyar daliban ta dauka musamman domin labarin da suka ji cewa a Abuja gwamnati tace a tsare shugabar makarantar Cibok wurin da aka sace 'yan matan.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.