Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me 'Yan Boko Haram Suke So?


Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram a bama, Fabrairu 20, 2014.
Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram a bama, Fabrairu 20, 2014.

Akwai rashin fahimta akan ko su waye Boko Haram, da kuma manufarsu a dai-dai lokacin da suke cigaba da tayar wa mutane hankula.

Biyo bayan fashewar bom a birin Abuja wanda ya kashe mutane kusan 80, da kuma sace dalibai mata sama da 200 a garin Cibok dake Jihar Borno, nazari ya koma kan fahimtar ko mene ne manufar ‘yan bindigan dake kashe mutane da kona gidaje musamman a arewa maso gabashin kasar, wadanda aka fi sani da Boko Haram.

Bello Habeeb Galadanchi na sashen Hausa yayi hira da dan Majalisar Wakilai na Tarayya mai wakiltar mazabun Marte da Monguno da Nganzai a Jihar Borno, Alhaji Muhammad Tahir Monguno inda ya tambaye shi ko me ‘yan Boko Haram suke so?

Tahir Monguno: Ainihi da aka fara maganar Boko Haram, tun lokacin da aka kashe su Muhammed Yusuf, to a lokacin manufansu su kafa mulkin da za’a gabatar da ita bisa ga addinin Islama, shine manufansu da fari, amma yanzu mutanen da suke da irin wannan manufa kuma suna da wannan akida, gaba dayansu, cikin kashi 100, ina ji kashi 95 babu su, sun riga sun rasa rayukansu. Yanzu abun gaba daya ya koma wani ta’addanci ne kawai, babu akida yanzu, ta’addanci ne kawai akeyi. Idan ba haka ba, ina maganar sato mata da addinin Islama? Ina maganar kashe mutane da addinin Islama? Ina maganar kashe mutane a cikin masallaci da addinin Islama? Yanzu abunda akeyi ta’addanci ne kawai. Yara ne matasa, wadanda babu abunyi wanda an same su an basu bindiga ana ta’addanci.

Bello Habeeb Galadanchi: An same su? Wane ne ya basu bindiga?

Tahir Monguno: Abunda yasa bindiga yayi yawa, ka san faduwar Gaddafi a Libiya, lokacin yakin gaddafi, ai wadannan bindigogin da yawa an ciresu, an baiwa Azbinawa da wadansu mutanen Mali saboda su taimakawa Gaddafi. Bayan rasuwar Gaddafi, bayan faduwar Gaddafi wadannan makaman suna hannu n mutane, wadanda basu da alaqa da gwamnati. Kuma da zarar ka bar Libiya, Nijar ne, da ka bar Nijar, Najeriya ne. Iyakar Najeriya kuma babu tsaro sosai. Ta wadannan iyaka mara tsaro aka samu, aka kawo wadannan bindigogin.

Tashe-tashen hankula dake da alaqa da Boko Haram ya samo asali ne tun shekara ta 2009, a lokacin da jami’an Najeriya suka kashe shugaban kungiyar Muhammed Yusuf ba tare da shari’a ba. Tun wannan lokaci ake samun kashe-kashe da kone-konen wurare a duk fadin arewacin Najeriya.

A baya-bayannan, musamman bayan fitowar wani sojan Najeriya wanda yace akwai sojojin Najeriya a cikin Boko Haram, ‘yan siyasa da dama na yin tambayoyi game da kungiyar, da kuma samun hannun gwamnati a cikinta.

Ko a baya-bayannan, Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya zargi Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da yiwa mutanen arewacin Najeriya kisan kiyashi, zargin da hukumomi suka karyata. Yanzu dai gwamnan ya dauki alwashin tattara takardun shaidu domin kai karar Jonathan a gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague dake Netherlands.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG