Wani mazaunin garin wanda muka saye sunnanshi saboda dalilin tsaro ya gaya mana cewa “an kaisu gaba da Makaifa, sauran matan wadanda suka gudu sune suke bamu labarin inda suke.”
“Jami’an tsaro tunda abun ya faru, basu samu sun je wajenba. Shiyasa iyayen yara suka yi zuciya, suka ce ko da za’a kashe su, gwara su bi sawun yaransu. Da suka je kusa da inda suke, sai aka ce musu ‘wadannan mutanen sun fi karfinku’, sai dai ku koma. Shine mutanen suka juya suka koma gida,” a cewar mazaunin garin Cibok din.
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tambaye mutumin dan Cibok ko me ya sani game da wadansu daga cikinsu da suka kubuto?
“An kara samo mata guda biyu wadanda suka kubuto, ko da matan suka zo, sune suka bada labarin inda (sauran) suke. Kuma sun gaya musu su ci abinci su koshi, saboda zasu dauke su, su tafi dasu zuwa wajen laraba,” inji mazaunin garin na Cibok.
Jami’an tsaro sun ji wadannan bayanan, amma basu yi komai ba, a cewar mazaunin Cibok din da baya so a bayyana sunansa.
Daliban mata su 234, ‘yan ajin karshe ne dake rubuta Jarrabawar Fita daga Sakandare a Yammacin Afirka, ko WAEC a takaice a lokacin da ‘yan bindiga suka kaiwa makarantarsu farmaki cikin daren Litinin, sama da makonni biyu kennan, inda suka kona makarantar mallakar gwamnati baki dayanta, sannan suka kwashe daliban a cikin manyan motoci suka tafi dasu.
Hukumar tsaron Najeriya, ta bakin kakakinta Chris Olukolade ta fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban, kalamun da iyaye da hukumomin makaranta suka musanta, kuma daga baya hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu dai bata sake bayanna wani mataki ko daya ba, akan irin aikin da takeyi na gani ta ceto daliban.
Shugaba Jonathan ya gudanar da taro Alhamis dinnan da duka gwamnoni, da shuwagabannin al-umma, da hukumomin tsaro game da batun tsaro, inda taron ya kayyade da bayanna matakai da za'a dauka domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Iyaye da ‘yan uwan daliban sun yi kokari da kansu su ceto matan, ta hawa babura sama da 150 domin bin sawun ‘ya’yansu, amma an gargade su akan cewa mutanen da suka sace daliban na dauke da makamai. A farkon makonnan ne kungiyoyin mata da iyayen sun yi taro suna kira a sako daliban. Wasu iyayen ma sun kuduri aniyar suyi zanga-zanga a Cibok domin nuna bacin ransu akan abunda suka kira rashin kulawa da lamarinsu daga hukumomi da jami'ai.
Gwamnatin Jihar Borno tayi alkawarin bada tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada wani bayani da zai kai ga ceto yaran mata.
A baya-bayannan ma, Gwamnan daya daga cikin jihohin dake da dokar-ta-baci, wato Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya zargi da hannun gwamnati a rincabewar lamuran tsaro a arewarin Najeriya, zargin da gwamnati ta musanta, kuma wasu shuwagabanni a Najeriya da dama suka yi ta sukan gwamna Nyakon. Har yanzu tsohon hafsin rundunar sojin ruwa bai janye kalamunsa ba, wanda a ciki harda tattara shaidu na kaiwa kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa a birnin Hague, domin tuhumar Shugaba Jonathan da kisan kare dangi.
Jihar Borno dai na daya daga cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, inda ‘yan bindigar nan da aka fi sani da Boko Haram suke da karfi, wadanda suka fara tayar da kayar baya tun shekara ta 2009. Ya zuwa yanzu gwamnatin Najeriya tace zata shawo kan matsalar, amma kashe-kashen mutane da kone-kone bai tsaya ba.
A kwanakin baya, 'yan siyasa sun bayanna cewa Shugaba Jonathan na so ya sabonta dokar-ta-baci, amma 'yan majalisar na daura dammarar adawa da hakan.