“Saboda haka mu (malamai) ba abokan shawararsu (shugabanni) bane, kuma idan mun bada shawara basa karba. Babu gaskiya, idan ba haka ba, yaushe za’a saci ‘yan mata fiye da 200 da wani abu, a tafi dasu lafiya lau, ba sama akayi dasu ba, ba nitsewa aka yi dasu ba, amma ace har yanzu ba’a gansu ba? Sati na uku? Wannan rashin tsaron yayi yawa,” a cewar Sheikh Dahiru Bauci. “Rashin kwanciyar hankalin yayi yawa a Najeriya, sai dai Allah Ya canza mana.
“Ubangiji Yace dukkan bala’i da ya sauka, akwai dalilinsa. Mutanen kasa su suka tsokano bala’i, bala’i ya sauka akansu,” a cewar Sheikh Dahiru Bauci.
Yanzu dai anyi kusan makonni uku da sace daliban mata su sama da 200 a makarantarsu ta Sakandare dake Cibok a Jihar Borno, a lokacin da suke rubuta jarrabawar fita daga makaranta. Kiyasin yaran na karuwa, saboda ba daliban makarantar ne kawai a cikin makarantar ba a lokacin da wannan lamari ya faru. Akwai daliban wasu makarantu, wadanda iyayensu suma suke korafin rashin ganin yaransu.
Ya zuwa yanzu, hukumomin Najeriya basu sanar da iyayen wadannan yara halin da ake ciki ba, batun neman yaransu, amma a kwanakin baya, kakakin ma’aikatar Tsaron Najeriya Chris Olukolade ya fitar da sanarwar da tace an kubutar da wadannan yara kusa dukkansu, daga baya kuma ya janye kalamunsa.