Shugaban Makarantar Sakadare ta Mata a Cibok, Asabe Kwanbura tace 32 daga cikin ‘yan matan sun kubuto, karin adadi kennan daga dalibai 20 da aka bada rahoto Alhamis dinnan.
Kwamishinan ilimin jihar ya tabbatar da wannan kiyasi, inda Juma’ar nan, yace an samo yaran su 32.
Yaran dai, su 129 ne ake kyautata zaton suke cikin makarantar a lokacin da ‘yan bindiga dauke da makamai suke je safiyar Talata suka kwashe matan a cikin manyan motoci. Yaran dai sun koma makarantar ne domin rubuta jarrabawar karshe wato WAEC, saboda makarantar tana daya daga cikin makarantun da aka rufe a watan Maris saboda dalilan tsaro.
Shedkwatar Tsaro ta bada wata sanarwar Larabannan cewa an ceto mafi yawancin ‘yan matan, guda takwas ne kawai ba’a san inda suke ba. ‘Yan uwan daliban da malaman makarantar sunce karya ne. Har yanzu ba’a san inda mafi yawancin ‘yan matan suke ba.
Kakakin ma’aikatar ya bada sanarwa a yammacin Alhamis, inda ya canza abunda ma’aikatar ta fada a baya, yana mai cewa bayanan da aka fara bayarwa suna da tangarda, kuma ba niyyar ma’aikatar bane ta yaudari jama’a.
Wannan rashin gaskiya dai ya kara akan rashin yarda da sojojiin da jama’a suke kara yi, kuma rundunar na cigaba da shan suka akan yadda take takalar yaki da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya.
Kwamishinnan ilimi a jihar Borno, Musa Inuwo Kubo ya gaya wa Muryar Amurka cewa wannan rashin gaskiya da sojojin suka yi ya kara akan rashin hakuri iyayen da kuma rashin yadda da hukumomin Najeriya.