Amuna Khadi: Batun Cibok dinnan, gaskiya mu mata abun ya shafe mu, kuma muna cikin bakin ciki. Abunda zan iya fada, ni har yanzu ina ganin Shugabannin Sojoji ne basu sa himma sosai kan aikinsu ba. Domin yanzu abunda yaka faruwa, mun shiga sati na uku kenna. Da ace sun saka himma, sun baro Abuja, sun dawo Maiduguri, sun shiga cikin wannan dajin, da yanzu tun-tuni an gano wadannan daliban, an dawo dasu gidajensu.
Amma babu yanda za’a yi shugabannin sojoji su zauna a Abuja a cikin ofis, wai suna bada umarni a je ayi kaza da kaza. Idan har suna tsoro su kadai suje Maiduguri, suzo su kira mu duk matan Najeriya, walLahi a shirye muke zamu iya binsu muje cikin dajin mu kawo ‘ya’yanmu cikin gida.
Ba dai-dai bane, yanzu da ace akwai ‘ya’yansu a cikin wannan abun, baza su zauna ko minti daya ba, da tuntuni an je a kwato su.
Bello Habeeb Galadanchi: Akwai korafe-korafen dake cewa ku shuwagabanni mata baku cewa komai a wadannan rigingimu.
Amuna Khadi: Mun fada, duk wanda yace bamu fadan komai ba dai-dai bane, a floor a cikin majalisa mun yi magana. Yanzu haka a Abuja akwai mata da suka zo, suna nan suna zanga-zanga, suka ce baza su bar nan wajen ba, sai sun ga an kwato dalibannan an dawo dasu gida.