Kalamun Kema Chikwe ke da wuya, jama’a suka fara mayarda martani.
Bashir Yusuf Ibrahim shine shugaban PDM na kasa, wanda ya bayyan alhininsa ga kalamun Chikwe, yana mai cewa bai kamata ace mace kamarta tayi wadannan kalamai ba.
Shima tsohon kakalin majalisar wakilan Tarayya, Alhaji Ghali Umar Na Abba ya nuna rashin dadinsa game da kalamun na Chikwe, inda yace kalamunta ba dai-dai bane.
Yanzu dai an share sama da makonni uku da sace daliban mata su sama da 200 wadanda ke rubuta jarrabawar karshe a makarantarsu ta Sakandare dake garin Cibok a Jihar Borno, a lokacin da ‘yan bindiga suka sace su.
Iyaye da ‘yan uwan daliban sun samu rahotanni daga sassa daban-daban na Jihar Borno, dake cewa an ga matan a cikin motoci ‘yan bindiga suna yawo dasu, kuma wasu daga cikin daliban da suka kubuto sun bada labarin inda ‘yan uwansu suke, amma jami’an tsaro basu kai daukin ceto yaran ba ya zuwa yanzu.
A kwanakin baya, kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya Chris Olukolade ya bada sanarwar ceto kusan duka daliban, amma bayan fusata daga iyaye da hukumomin makarantar, hukumar tsaron ta janye kalamunta. Ya zuwa yanzu bata ce ga matakan da take dauka ba wajen ceto wadannan yara.