Wani mai magana da yawun daliban mai suna Fahd Abbas Jega, ya shaida ma abokin aikinmu Bello Habib Galadanchi cewa tausayi da dan'uwantakar da ke tsakanin daliban ne dalilinsu na mara ma takwarorinsu 'yan asalin Nijeriya wajen yin wannan zanga-zanga ta lumana.
Ya ce dalibai 'yan Nijeriya sun kadu sosai da jin labarin sace dalibai mata a makarantar Chibok a jihar Borno; don haka sai su ka yanke shawarar shirya wannan zanga-zangar lumana da hadin gwiwar wasu dalibai 'yan asalain kasashen Masar da Sudan na bukatar a maido da daliban da aka sace a Nijeriya.
Malam Fahd ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zangar ce bisa shawarar Shugaban kungiyar daliban Nijeriya na Kwalejin mai suna Faisal Abdullahi Jaram. Wasu daga cikin kwalayen da su ka daga na dauke da sakon cewa, "A Maido Ma Na Da Dalibai Mata 'Yan'uwanmu." Baya ga daga kwalayen, zanga-zangar ta kuma hada da yada wannan bukatar a dandalin sada zumunci na intanet don a sani sosai.