Uwargidan gwamnan jihar Bornon Hajiya Nana Kashim Shettima ta kira wani taron gaggawa a fadar gwamnatin jihar domin tattauna hanyoyin da za'a bi a kubuto daliban. Kawo yanzu babu wanda ya san halin da suke ciki. Mata da dama da suka tashi su yi jawabi akan hanyoyin da za'a bi sun yi hawaye.
Yayin da take jawabi da matan tace ta kira taron ne domin sace 'ya'yansu da wasu 'yan bindiga suka yi. Tace matsalar ba abun damuwa bane kawai abun bakin ciki ne. Lokacin da take jawabi matar gwamnan sai ta bige da kuka. Ta shaidawa matan su manta da batun kabilanci ko banbancin siyasa su fuskanci matsalar dake gabansu. Tace ta san zasu iya kuma Allah Yana tare da su.
Bayan an kammala taron Muryar Amurka ya zanta da shugabannin wasu kungiyoyi mata da suka halarci taron.Wata Esther tace shiri da iko suna wurin Allah. Tace magana ce dake bukatar addu'a. A cigaba da addu'a tare da azumi ba dare ba rana. Ita ma Hajiya Halima Abubakar ta kira 'yan bindigan su ji tsoron Allah su saki 'yan matan cikin koshin lafiya. Ta kira a yi addu'a dakuma rokon Allah akan zaman lafiya. Duk shugabannin kungiyoyin mata da suka yi magana sun roki 'yan bindigan su ji tsoron Allah su sako daliban.
Ga karin rahoto.