Bisa duka alamu zanga-zanga da batutuwa akan 'yan matan da aka sace a garin Cibok ba zasu kare ba muddin ba'a sako yaran ba. Lamarin ma ya kara kamari domin kungiyar Boko Haram ta fito karara tace ita ce ta sace daliban.
Jiya a birnin Legas mata sun yi zanga-zangar lumana inda suka kira lallai a sako yaran. Matan sun bada shawara cewa Musulmi da Kirista su yi azumi na musamman sabili da a samo yaran. Wadda ta jagoranci zanga-zangar tace duk da yake mun yadda da shugaban kasa amma abun da muke cewa ya kara kaimi wajen neman yaran. Sun ce wannan ba shi ne farko ba domin a can baya har yanka yara aka yi.
Yayin da mataimakiyar gwamnan Legas ta karbi masu zanga-zangar tace zasu yi duk iyakan abubuwan da zasu iya yi domin su taimaki gwamnatin tarayya akan lamarin.
Zanga-zangar bata tsaya a Legas kadai ba a kudancin Najeriya domin mata a Abeokuta fadar gwamnatin jihar Ogun su ma sun yi tasu. Uwargidan gwamnan jihar Madam Amosun ita ce ta jagorancin zanga-zangar. Yayin da gwamnan ke karbarsu uwargidansa tace bamu san inda wanna lamari zai kai ba. Yau diyan wasu ne amma gobe lamarin ka iya kasancewa akan namu 'ya'yan. Ta roki gwamnan da Allah ya taimaka masu a kawo karshen wannan mugun abu.
A Calabar fadar gwamnatin jihar Cross Rivers haka ma lamarin ya kasance. Ban da mata har yara matasa 'yan mata suka shiga zanga-zangar inda suke sanye da bakaken kaya. Wata da tayi magana tace sun zo ne domin su fadawa wadanda suka sace 'yanuwansu mata da su sakesu.
Ga karin bayani.