Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Kai Jonathan Kotun Manyan Laifuka ta ICC - inji Nyako


Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako.
Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako.

Gwamnan jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako mai ritaya a wata wasika da ya aikawa kungiyar gwamnoni arewacin Najeriya, yace lallai akwai abin dubawa game da wasu abubuwan da suka faru cikin cikin kwanakinan.

Kama daga harin bom na Abuja da sace yara mata ‘yan makaranta a Cibok dake jihar Borno dama kashe-kashe ko yunkurin kashe sarakuna, malamai, shuwagabanin addini da na siyasa ciki harda shugaban majalisar dattawa da wasu gwamnoni.

Murtala Nyako yayi wannan furuci ne a hiran da yayi da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz inda yace ”in ka dauki sojoji mu na Najeriya, sojojin na kusa a raba su biyu ne akwai wadanda ake shigo dasu da rana tsaka aje a sasu a wani brigade ko wani unit brigade kwamanda ma baida wani izini a kansu kuma kaga wanna zai zamanto su ake turawa suna karkashe mutanen mu, ko yaran mu da suke soja yau. In kaje ka bi salsala wanda aka kashe ta baya aka harbe shi, domin inde mutun mai tsokanaka ne in kazo gabansa kake harbi to yawancin yaran mu da suke kashewa ta baya suke kashe su sai ya juya yana tsammanin wani maigadansa ne ke bayansa ashe ba maigidansa bane ko kuma abokin aikinsa ne a bayan sa wani ne wanda yake son kashe shi sai ya buga masa dalma kurum a jiki.”

A martanin da fadan shugaba kasa ta fitar dake dauke da sa hannu mai taimakawa shugaban kasa ta fuskar harkokin yada labarai Doyin Okupe, shugaba Goodluck Jonathan ya zargi gwamna Adamawa da yunkurin raba kawunan ‘yan Najeriya ta hanyar ingiza ‘yan arewa don kyamar gwamnatin PDP, shugaba Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da su yi fatali da kalamain gwamnan Adamawan.

Wani masanin harkar tsaro Dr. Bawa Abdullahi Wase yace akwai abun dubawa akan wasika da Murtala Nyako ya rubuta.

Dr. Bawa yace ”Nyako bawai kadai tsohon soja bane saida ya zama shugaban sojajin ruwa na Najeriya bayan haka ya taba yin gwamna ma yana soja, indan ka duba shekarun Murtala Nyako ka duba shekarun Obasanjo ka kuma duba shekarun duk wani soja a yau wanda ke da mukami, yake wurin sai ka tambayi kan a lokaci da Murtala Nyako Yake rike da wanna mukamin ko shugaban kasa yake dashi su manene girmasu a soja, sai ka duba shugaban shi kansa a lokaci da Murtala Nyako yayi gwamnan sa na farko manene shekarun shugaban kasan na yanzu a duniya? Don haka mahaukaci ne kawai wanda tunaninsa ya mauje zai dauki maganarsu maganar banza, kuma zan baka misali biyu a gurguje na farin farko indan da babu hannun gwamnati a abubuwan da ya faru a Abuja, ina tabbatar maka da shugaban kasa ba zai zo kafin wadannan mutane suce sune suka yi, ya kira sunan cewa boko haram ba domin na biyu kenan da yayi wannan, domin a 1/10/2010 mutane garin shi sun buga bom a Abija a Eagle Square minti bakwai bayan su kace su suka yi, ya gayawa duk duniya ta gidajen rediyo cewa sam ba mutane sa bane."

Yanzu dai kamar yanda gwamnar Adamawan ya tabbatar an fara tattara bayanai domin gurfanar da shugaba Jonathan a kotun duniya domin tuhumarsa da laifin kisan kare dangi.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG