Game da Mu
Game da Mu
Muryar Amurka ta VOA itace kafar watsa labarai ta kasa-da-kasa mafi girma a Amurka, wacce ke watsa shirye-shirye a cikin harsuna 45 zuwa ga al’ummar duniya dake da karancin kafafen watsa labarai da ma wadanda basa da su. Ita wannan kafar ta VOA, wacce aka kafa ta a shekarar 1942, kafa ce da ta sadaukar da kanta wajen samarda ingantattu, cikakku da kuma kamalallun bayanai da labarai wadanda kuma ake tsage su akan akidar gaskiya komai dacinta. Mutanen Amurka masu biyan haraji ne ke samarda dukkan kudaden da ake anfani da su wajen gudanarda aiyukkan wannan tashar ta VOA, wacce reshe ce ta Hukumar Kafafen Watsa Labarai na Gwamnatin Amurka, wacce a takaice ake kira USAGM.
Aiyukkan da VOA ke gudanarwa tareda ‘yancinta na yin tankade-da-rairayen bayana da take watsawa, ana gudanar da su ne a karkashin dokokin da ke kare ‘yanjaridun VOA daga duk wani tasiri, matsin lamba ko martanin ma’aikatan gwamanti ko na ‘yan siyasa.
A shekarar 1976 ne shugaban Amurka, Gerald R. Ford ya rattaba hannu akan Kundin Manufofin VOA wanda ya tanadi cewa:
1. Jidaddun, VOA zata zama wata kafar watsa labarai masu inganci da ake iya dogara a kansu. Duk labarun VOA zasu kasance daidai ne, na adalci kuma cikakku.
2. VOA zata wakilci Amurka baki dayanta, ba wai wani bangare na Amurka ba, saboda haka zata gabatarda manufofi kamallalu, na dukkan bangarori kuma cikakku da zasu fayyace matsayi da tunanin aksarin mutane da cibiyoyin Amurka.
3. VOA zata gabatarda manufofin Amurka a bayyane kuma cikin kuzari, kuma zata zama hurumin gabatarda muhawara da tattaunawa akan batutuwan dake da tasiri da wadanan manufofin.
A shekarar 1994 ne Majalisar Dokokin Amurka ta amince da Dokar kafa Hukumar Gidajen Radio da Telebijin ta Amurka, USIB. Wannan dokar ta tanadi cewa wajibi ne dukkan aiyukkan ‘yan-jaridun VOA zasu kasance masu madafa, daidai, bisa adalci, cikakku, masu bayyana ra’ayin duk wadanda batu ya shafa kuma wadanda ke wakiltar tafarkin al’adu da halin zaman jama’ar Amurka na jinsuna iri daban-daban.
A shekarar 2016 ne kuma majalisar Dokoki ta sake tabattarda Dokar Hukumar Tsaro wacce ta tanadi cewa dole dukkan aiyukkan ‘yan-jarida da bada rahottani su ci gaba da zama wadanda ake gudanarwa a bisa akidar cikakken ‘yancin kai da kuma akidar adalci.
A kowace rana, ‘yan-jaridar dake wa VOA aiki na ci gaba da aiki tukuru don tabattarda ganin suna aikin a bisa akidojin ‘yan jaridu masu cin gashin kansu na duniya.
VOA
Kafar Watsa Labarai Mai Cin Gashin Kanta Na Da Matukar Muhimmanci