WASHINGTON, DC —
Mutun na baya bayan nan da yayi wannan kira shine shugaban kungiyar IZALA ta Tarayyar Najeriya Sheik Sani Yahaya Jingir.
“To abinda Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah zata kara fada shine, don dama ina fada, da sauran malumanmu cewa duk ana fada cewa ‘duk kasa ta duniya, tana da shugabanni na Kasa, tana da shugabanni na tsaro, tana da sarakunanta, tana da malumanta, tana da ‘yan siyasarta, tana da majalisu a kasar, kuma ba an yi sune su zama basu da aikin yi ba”, a cewar Sheikh Jingir.
“Don haka muke kira ga Ofishin fadar Shugaban Kasa a Najeriya cewa sunansa a turancin Ingila ana ce masa ‘Kwamanta In Cif’, duk yanda za’a yi tsaron kasa babu yadda za’a ce babu hannunsa,” Sheikh Jingir ya cigaba da cewa.
Sheikh din yayi karin bayani “to idan aka ce ga wani, an shiga kasarsa an kama ‘yan mata dari kaza, dole muce to kai shugaban kasa me kake yi? Ku ‘yan Majalisu me kuke yi? Ku sarakuna me kuke yi? Ko sojoji me kuke yi? Ku ‘yan sanda me kuke yi? Idan da kuna bacci ne, to mu a Izala zamu ce ku bar bacci ku tashi, kuyi aikin da Allah Ya dora muku don Allah."
Har yanzu dai ba’a gano daliban sama da dari biyu da aka sace a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe, amma wasu kusan 40 sun kubuce daga hannun ‘yan bindigan da suka sace su.