Saboda hakan ne, ‘yan Najeriya musamman ‘yan shiyyar arewa maso gabas, sun soma tofa albarkacin bakinsu.
Wani mai suna Gaini Adamu yace “ina yiwa mutanen Najeriya farin ciki da albishir dangane da cire Ahmed Gulak da akayi daga mukaminsa. Duka abinda yayi farko zai ga karshe.”
Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin Ahmed Gulak, amma bai dauka wayoyin da aka buga mishi ba, sannan bai amsa sakonnin Text da aka aika masa ba.
Mallam Gaini Adamu ya bada shawara ga iyayen daliban Cibok da ‘yan bindiga suka sace, akan suyi zaman dirshen a kofar fadar shugaba Goodluck domin ya fito musu da ‘ya’yansu.
Idan ba’a mance ba, wasu kungiyoyin iyayen yaran sun gudanar da zanga-zanga a birnin Abuja domin gani an fito musu da 'ya'yansu.