A karshen taron ana sa ran za’a dauki matakai na bai daya tsakanin gwamnatin tarayya, da na jihohi, da manyan jami’an tsaro baki daya domin hawa kan alkibila guda daya domin takalar matsalar tsaro da ya addabi Najeriya.
Idan ba’a manta ba, yanzu sama da makonni biyu kennan da fashewar Bom a wata tashar motar dake unguwar Nyanya dake birnin na Abuja, da kuma sace dalibai mata sama da 200 a makarantar sakandare dake Cibok a jihar Borno wanda ya fusatar da jama’a matuka. Bugu da kari yaki dake faruwa a halin yanzu tsakanin gwamnati da kungiyar ‘yan tawaye da aka fi sani da Boko Haram arewacin Najeriya.
Duk wani yunkuri na gani tsaro ya karu daga wajen gwamnati ya ci tura, kuma manazarta da mashawarta na gani kamar gwamnati bata iya kokarinta domin gani rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya an kare su.