Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Rufe Aiki a Abuja


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Shugaban Faransa, Hollande.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Shugaban Faransa, Hollande.

Saboda da taron Tattalin Arzikin Duniya da za'a yi a birnin Abuja a makon gobe, gwamnati ta bada sanarwar rufe duka makarantu da ayyukanta.

Taron da za'a share kwanaki uku ana yi, wanda za'a yi a makon gobe shine dalilin rufe duka makarantun dake birnin Tarayya, tare da rufe wuraren ayyukan gwamnati domin maganin 'cinkoso' a cikin gari.

Alhamis dinnan ne wani Bom ya fashe a Nyanya dake Abuja, kusa da wajenda Bom na farko ya tashe kusan makonni uku kennan, kuma yayi sanadiyar rayuka sama da 70 da raunata sama da mutum 100. Wannan hari na Alhamis yayi sanadiyar rayuka kusan 17 da raunta sama da 60.

Matsalolin rashin tsaro yafi yawa a arewa maso gabashin kasar yanzu ya samu kansa a babban birnin Tarayyar, wajenda a halin yanzu mata da iyayen dalibai wadanda aka sace a makaratar Sakandare dake Cibok suka gudanar da zanga-zangar lumana suka cewa gwamnati ta gaza wajen tsare rayuka da ceto dalibai wadanda aka sace.

A kwanakin baya, an tsaurara matakan tsaro a birnin na Abuja, lamarin da ya saka 'yan majalisa da jama'a suka yi ta tsokaci.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG