Kungiyar matasan arewa ta tsayar da lokacin da zata yi gangami zuwa dajin Sambisa domin kwato daliban da aka sace indan har gwamnati ta kasa kwatosu.
WASHINGTON, DC —
Shugaban habbaka rayuwar matasan arewa Imrana Wada Nas yace idan ba'a ji duriyar daliban da aka sace cikin makon nan ba matasan arewa a shirye suke su kwato 'yan uwansu da aka sace daga Cibok.
Da yake bayani Imrana Wada Nas yace dukansu sun baro garuruwansu, sun baro ayyukansu domin su hadu su yi zanga -zangar shiga dajin Sambisa. Sun sa lokacin da zasu yi taro na karshe domin su tabbatar sun tafi sun taho da 'yan uwansu tunda gwamnati bata iyawa. Lokacin da zasu tafi ko carbi ba zasu dauka ba. Babu wani makami babu komi haka zasu yi gangami su tafi. Zasu fara daga makarantar kana su bi a hankali har su je su samesu.
Inji Imrana Wada Nas abubuwan da 'yan Boko Haram ke yi ba addini ba ne kuma ba tarbiya ba ce irin ta mutanen arewa. Wasu al'adu ne aka dauko wadanda basu da tasiri. Duk da sadakin da suka ce sun basu na nera dubu biyu, Imrana yace shin wa yace sadaki nera dubu biyu ne. Auren da suka ce sun yi bai cika ba domin babu bangaren iyayen daliban.
Shugaban kungiyar kananan kabilu Mr. Mark Amani yace yana da ayar tambaya akan kwamitin da shugaban kasa ya kafa na sasantawa da 'yan kungiyar Boko Haram. Shin wai su wanene kuma da wanene suke zama. Idan suna zama da shugabannin Boko Haram to a fito dasu fili kowa ya ga fuskokinsu domin su ne basa son Najeriya ta zauna lafiya kuma su ne suke hallaka mutane. Yace idan ba za'a fito a fadi gaskiya ba to duk yaudara ce.
Ibrahim Garba Wala na bangaren taron matasan jihohin arewa yace gazawar gwamnati da kuma korafin rashin makamai na ba kungiyarsa mamaki. Hafsan hafsoshin da ya sauka wato Ihejirika yace an kashe makudan kudi domin sayen makaman yaki da ta'adanci to amma makaman ba'a gansu ba domin sojoji suna kukan babu kayan aiki. Shin ina makaman da aka saya suke. Yace sun ga dalibal suna makaranta an yankasu, wasu kuma an sacesu.
Amma Chinedu Okpalamma yace shugaba Jonathan yana matukan kokarin kwato daliban domin ya ba duk jami'an tsaro goyon baya sabili da shawo kan wannan kalubalen.
Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5