Labaran Maku Dangane da Cibok

Labaran Maku

Yanzu sama da mako biyu kennan da sace dalibai mata sama da 200 da 'yan bindiga suka yo awon gaba dasu daga garin Cibok dake Jihar Borno, iyaye na jiran hukomomi suyi musu bayani. A kwanakin baya, majalisar zartaswar Najeriya, tayi taronta a Abuja inda ministan labarai Labaran Maku yayi bayani.
Mr. Maku yace jami'an tsaro suna aikinsu domin a ganosu a kuma mayarda su gidajen iyayensu. Shugaban kasa ya riga ya bayarda umurni kuma ana kan yin aikin. Yayi addu'ar Allah Ya bada nasara akan miyagun mutanen dake muguwar aika-aika. Yace mutanen sun watsar da duk dokokin Allah na kowane addini. Babu shakka shedan su ke yiwa aiki. Yace babu wani addini da yace a kama yara mata a shiga daji da su.

Da wakilin Muryar Amurka ya gayawa ministan cewa abun mamaki ne a ce 'yan bindiga sun shiga makarantar sun yi sa'o'i hudu suna kama yara suna sasu cikin motoci amma babu ko jami'in tsaro daya da ya je wurin, sai ministan yace rahotannin da 'yan jarida ke ji ke nan.

Ministan ya juya kan 'yan jarida inda yace labaran da suke bayarwa sukan karya gwiwar jami'an tsaro. Yace suna magana ba tare da tabbatar da an samu zaman lafiya ba.

Yanzu dai jama'a a sassa daban-daban na Najeriya da ma ketare, na zanga-zangar lumana suna kira ga gwamnati akan ta dauki matakin nemo wadannan dalibai, musamman ma bayan fitowar sanarwa daga kakakin ma'aikatar Tsaron Najeriya, Chris Olukolade wanda yace an kubutar da kusan duka daliban, daga baya kuma hukumar ta janye kalamunta.

Duk da cewa Labaran Maku yace jami'an tsaro na aikin gano wadannan yara domin mayarwa iyayensu, hukumomi basu bada tabbacin sanin inda daliban suke ba, kuma iyayen basu ji komai daga gwamnati ko hukumomin tsaro ba.

Matsalar tsaro na cigaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya, wanda hakan yasa shuwagabanni suke kokarin gano daga inda matsalar take.

A baya-bayannan, Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako ya dauki alwashin tattara takardun shaida domin kai karar shugaba Goodluck Jonathan a gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa dake birnin Hague. Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.