Jagoran sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi wa wasu firsinoni afuwa bisa la’akari da sharudan da dokokin shari’ar kasar su ka tanada, matakin da jami’an kare hakkin dan adam suka yi na’am da shi ganin yadda abin zai taimaka a rage cunkoso a gidajen yari.