Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamomin Babbar Gogayya Tsakanin Amurka Da Rasha Sun Bayyana A Nijar


Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da karamin ministan tsaron kasar Rasha Colonel General EVKOUROV LUNUS BEK
Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da karamin ministan tsaron kasar Rasha Colonel General EVKOUROV LUNUS BEK

Sabuwar jakadiyar Amurka ta gabatar wa hukumomin rikon kwaryar Nijar takardun kama aiki, kwana daya bayan haka Rasha ta tura karamin ministanta na tsaro zuwa birnin Yamai, ziyarar da masana suka fassara a matsayin wani yunkuri na Rasha na samun matsuguni a Yankin Sahel.

Tun a watannin da suka gabata ne gwamnatin Amurka ta turo sabuwar jakadiyarta a Nijar, to sai dai juyin mulkin da aka fuskanta a kasar ya yi sanadin dakatar da dukkan wani shirin soma ayyuka a bisa dalilai masu nasaba da manufofin kasar da ke matsayin jagorar harkokin dimokradiyya a duniya.

Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da jakadiyar Amurka Ambasada Khatleen Fitzgibbon
Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da jakadiyar Amurka Ambasada Khatleen Fitzgibbon

Canjin matsayin da aka fuskanta a baya bayan nan dangane da wannan dambarwa ya sa sabuwar jakadiyar Ambasada Khatleen Fitzgibbon ta gabatar wa ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare kwafin takardun kama aiki a yayin wani kwarkwaryan buki da ya gudana a ranar Asabar. Matakin da masani a kan harkokin diflomasiya Moustapha Abdoulaye ke alakantawa da yaki da ta’addancin da Amurka ta sa gaba a yankin Sahel.

A wani abu da ke kama da rububin samun matsugunni, karamin ministan tsaron kasar Rasha Kanal Janar Yunus-bek Yevkurov ya sauka birnin Yamai a yammacin ranar Lahadi 3 ga watan Disamba, inda ya gana da ministan tsaro Janar Salifou Mody, wato kwana daya kenan bayan da jakadiyar ta Amurka ta gabatar wa hukumomin Nijar takardun kama aiki.

Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da karamin ministan tsaron kasar Rasha Colonel General EVKOUROV LUNUS BEK
Ganawar ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi da karamin ministan tsaron kasar Rasha Colonel General EVKOUROV LUNUS BEK

A cewar masana wannan wata alama ce ta sabon salon gogayyar da ke tsakanin manyan kasashen duniya a yau.

Kasar Rasha wace tun tuni ke da hulda da kasashen Mali da Burkina Faso a fannin tsaro, ta yi kaurin suna a idon kasashen yammaci sakamakon zarginta da amfani da sojan haya na kamfanin Wagner ta hanyoyin da suka saba wa doka.

Idan ziyarar karamin ministan tsaronta ta kasance ta neman kulla irin wannan hulda, to kam za ta yiwu a raba gari a tsakanin Nijar da dadaddun kawayenta na yammacin duniya, inji Pr Dicko Abdourahamane, malami a jami’ar Zindar.

Nan take dai ba a bayyana makasudin wannan rangadi ba, illa kawai aka kira abin ziyarar aiki. Dama tun a ranakun farkon farfado da mu’amula a tsakanin hukumomin Mali da na Nijar wasu ‘yan kasa ke hasashen yiwuwar samar da kusanci a tsakanin hukumomin mulkin sojan CNSP da na Rasha, kasar da ake ganin ta dukufa da yunkurin kama wuri a kasashe mambobin kungiyar AES.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG