‘Yan ta’addan wadanda ke kan babura sun isa kauyen na Maichilmi ne a wani lokaci da dalibai ke tsakar daukan karatu, a saboda haka suka umurci yaran da malamansu su fice kafin daga bisani su kona azuzuwan makarantar, bayan kammala wannan aika aika maharan sun kuma tilasta musu sauraren wa’azin da suka shirya.
Lokaci kadan bayan watsewar taron wa’azin labari ya kai wa jami’an tsaro da ke sintiri a wannan karkara, wadanda a take suka nufi inda abin ya faru suka fatattaki ‘yan ta’addan tare da hallaka 8 daga cikinsu, suka kuma kama bindigogi da babura. An dai ga gawarwaki jina jina a wasu hotuna da suka karade kafafen sada zumunta.
Mai sharhi akan sha’anin tsaro Dr. Abba Seidik, na mai fassara wannan galaba a matsayin wani somin tabin nasarorin da ka iya biyo bayan kwace garin Kidal daga hannun ‘yan bindigar arewacin Mali.
Fannin ilimi na daga cikin fannonin da matsalolin tsaro suka addaba a jihar Tilbaery mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso, inda ‘yan ta’adda kan yi wa malamai barazana har ma da sace wasu daga cikinsu, yayin da kona dakunan karatu ya zama ruwan dare a yankin, lamarin da a yanzu haka ya tilasta wa dubban yara zaman gida.
Galabar da jami’an tsaron Nijar suka samu a jiya Alhamis a kauyen na Maichilmi abin a yaba ne, inji sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Laouali Issoufou, wanda ya kara da tunatarwa kan muhimmanci ilimi ga kowace al’umma.
Nan take dai ba wata sanarwa a hukunce da ta tabbatar da zahirin abinda ya faru da jami’an tsaro a yayin kafsawar ta kauyen Maichilmi.
Saurari rahoton Souley Mumuni Barma:
Dandalin Mu Tattauna