Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sojojin Juyin Mulkin Nijar Ya Kai Ziyara Mali Da Burkina Faso



Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchianai
Shugaban majalissar sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijer Janar Abdourahamane Tchianai

Shugaban Majalissar Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani na ziyarar aiki ta wuni 1 a kasashen Mali da Burkina Faso a wannan Alhamis 23 ga watan Nuwamba.

Shugaban juyin mulkin ya kai ziyar ne da nufin tantaunawa da takwarorinsa a wani yunkurin karfafa hulda a tsakanin kasashen 3 makwaftan juna masu fama da matsalolin ta’addanci kuma dukkansu ke karkashin mulkin soja lamarin da ya haifar da tsamin dangantakar da ke tsakaninsu da kungiyoyin kasa da kasa da manyan kasashen duniya.

Wannan shine karon farko da jagoran sojojin majalisar CNSP ke kai ziyara wata kasar waje watanni 4 bayan kifar da shugaba Mohamed Bazoum. Sanarwar da ofishin kula da hidimomin gwamnatin Nijar ya fitar na cewa, a wannan rangadi zuwa Bamako da Ouagadougou, Janar Abdourahamane Tchiani na samun rakiyar ministan tsaron kasa, Janar Salifou Mody da Ministan wasannin motsa jiki kakakin Majalisar, CNSP Kanal Amadou Abdourahamane da Ministan harkokin wajen, Bakary Sangare da Ministan ayyukan yawon bude ido, Madam Soufiane Aghaichata da jakadun kasar a wadannan kasashe da wasu mukarabban fadarsa.

Dangantaka ta sake farfadowa a tsakanin kasashen 3 a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yuli har ma ta kai su ga kafa kungiyar kasashen yankin sahel wato AES da nufin hada karfi domin yaki da kungiyoyin ta’addanci da ma dukan wani al’mari da ke kama da barazana wa zaman lafiyar 1 daga cikinsu.

A albarkacin wannan sabuwar alakar ne gwamnatocin sojan Mali da Burkina Faso suka jaddada goyon baya ga Nijar lokacin da kungiyar CEDEAO ta yi barazanar amfani da karfin soja don fatattakar sojojin da suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

A hirarsa da muryar Amurka, dan fafutika Ibrahim Namewa ya ce ziyar abun alfahari ne kuma za a samu labaru masu dadi da za su amfani al'umma.

Lalacewar al’amuran tsaro na daga cikin manyan dalilan da soja suka bayar wajen kifar da gwamnatocin fararen hula a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, sai dai har yanzu ba ta canza zane ba a kan iyakar kasashen nan 3. Abinda ya sa dan takara a zaben shugaban kasa na 2020 Intinicar Alhassan ke kallon ziyarar ta Janar Tchiani a matsayin ta neman mafitar takunkumin ECOWAS da a dai gefe matsalolin tsaro.

Nijar ta taka rawa wajen kwato garin Kidal daga hannun kungiyoyin ‘yan tawaye da na ta’addancin arewacin Mali a tsakiyar watan nan Nuwamba abin da ya sa wasu masharhatan ke fassara ziyarar ta jagoran majalissar CNSP a matsayin ta neman sanin halin da dakarun kasar ke ciki bayan wannan gumurzu.

Mali na da alakar aiki da sojojin hayar kamfanin Wagner na Russia har zuwa yau, Nijar a na ta bangare na mu’amular ayyukan soja ne da sojoji gwamnatin Amurka da ke da sansani a arewacin kasar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG