Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Benin Ya Yi Wa Majalissar Dokoki Bayani Kan Rikicin Nijar


France Returning African Art
France Returning African Art

Shugaba Patrice Talon na jamhuriyar Benin ya bayyana aniyar sake da maido da hulda a tsakanin kasarsa da kasashe makwafta wadanda suka fada karkashin mulkin soja.

Ya na mai jaddada cewa shi da takwarorinsa na kasashen yammacin Afrika sun kakaba takunkumi ga irin wadanan kasashe ne a bisa manufofin kare dimokradiya da mutunta ka’idodin da dukkan kasashen yankin suka rattaba wa hannu.

Shugaban Patrice Talon da ke jawabi a zauren Majalissar Dokokin Jamhuriyar Benin a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, ya jaddada matsayin kasar dangane da matakin ladabtarwar da duniya ta dauka a kan kasashen da soja suka yi juyin mulki.

Yace dare karagar mulki da karfin bindiga abu ne da ya zama wajibi kowane cikkaken dan dimokradiya ya yi tir da faruwarsa. Yin haka abu ne da yake da tabbacin ya yi daidai da maunufofin kasarsa haka kuma abu ne da ya yi daidai da tsarin kasashen yanki da na nahiya da ma kasashen duniya baki daya.

Ya kuma kara da cewa Benin ba ta so ba , ba ta kuma taba fatan takunkumin da kungiyoyin kasa da kasa suka kakaba zai haddasa matsatsin rayuwar yau da kullum a wajen al’umomi.

Wannan ne ya sa kasarsa a asirce ta sha aika sakwannin zuwa ga wadanan kasashe, ‘yan uwa musamman kasar Nijar, domin a cewarsa ya yi imani akwai lokacin a yi Allah wadai, akwai lokacin tursasawa, akwai kuma lokacin yin bita a kuma yi na’am.

Shugaban Jamhuriyar Benin wanda ya bayyana bukatar ganin hulda ta dawo tsakanin kasarsa da kasashe makwafta inda soja suka yi juyin mulki, musamman Nijar, ya kara da cewa akwai alamar kauda kai daga bangaren hukumomin mulkin sojan wannan kasa ganin yadda har yanzu suke ci gaba da yin buris da kasashen duniya dangane da wannan dambarwa. Abin nufi magana ta rage daga garesu inji shi.

Kawo yanzu ba wani martani daga bangaren mahukuntan Nijar dangane da kalaman na Shugaba Patrice Talon.

Tsamin dangantaka a tsakanin hukumomin Jamhuriyar Benin da Jamhuriyar Nijar matsala ce da ta samo tushe daga takunkumin da ECOWAS ta kakaba a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Sai kuma uwa uba, batun harin da kungiyar ta yi barazana amfani da shi don mayar da hambararren shugaban kasa, Mohamed Bazoum, kan kujerarsa, matakin da a nan cikin gida jama’a ke zargin Benin da yin gaba-gaba wajen ganin ya tabbata.

Kuma dukkan wannan kace-nace na wakana ne a wani lokacin da kasashen 2 ke shirin kaddamar da aiyukan bututun man Nijar-Benin a watan gobe.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG