A sanarwar da suka fitar jim kadan bayan bayyanar labarin shawarwarin da taron shugabanin kasashen yammacin Afrika na ranar 10 ga watan disamban 2023, kungiyoyin kawancen Front Patriotique na FPSN sun fara nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira take taken kungiyar CEDEAO.
A hirar shi da Muryar Amurka, Bana Ibrahim, kakakin wannan gamayya, ya ce shuwagabanin sun shigo ECOWAS ba don komai ba, ila don samun cigaba, kuma yarjiniyar da aka kafa, ba ta ba ECOWAS dama ta dauki irin wannan matakai da ke gallaza wa kasar ba.
To sai dai dan Majalissar dokokin kasa Abdoul Moumouni Ghousmane na ganin alamun samun ci gaba a yunkurin warware wannan rikici.
Tsayin gwamen jakin da ECOWAS ta yi dangane da dambarwar siyasar Nijar abu ne da ke bukatar mahukunta su maida martani kansa a cewar Front Patriotique.
A nan dan majalissar ya gargadi hukumomin mulkin soja su yi buris da irin wadanan shawarawari.
Sauraren koke koken al’umma ko biya masu dukkan wata bukatar da suka zo da ita abubuwa ne da suka rataya a wuyan magabata to amma kuma wajibi ne a gudanar da lamura da tsinkaye inji masani kan harakokin diflomasiya Moustapha Abdoulaye.
Shugaban majalissar CNSP Janar Tiani da ke bayani a karshen makon jiya game da kace nacen da ke tsakanin CEDEAO da Nijar a wata hira da kafafen gwamnati, bai nuna alamun shirin ficewar kasar daga kungiyar ta kasashen yammacin Afrika b, a hasalima ya bayyana rashin jin dadi kan yadda kasashe makwafta ‘yan uwan juna suka bai wa kasashen yammaci damar ratsa su.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna