Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu karin bayanan da ke gaskanta zargin yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kudade da dama da wasu tarin kayayaki a fadar ta hambararren shugaban.
Wadansu kungiyoyin fararen hula masu goyon bayan sojojin CNSP a Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda suka ce gwamnan Yamai ya na masu katsalandan a harkokin cikin gida.
Kungiyoyin dai na zargin wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka da jefa al'umar Nijar cikin kangin wahalhalu sanadiyyar takunkuman da aka kakaba mata.
A Nijar, wasu kungiyoyin farar hula sun kafa hadaka mai lakanin DCTR da nufin taimaka wa gwamnatin sojan kasar a yunkurin neman mafita sakamakon takunkumin kungiyar CEDEAO, suna masu jaddada aniyar bada gudummowa a dukkan tsare tsaren da suka shafi yunkurin mayar da kasar kan turbar dimokradiyya.
Lauyoyin da ke kare hambararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum sun maida martani ga gwamnatin mulkin sojan kasar wace ta zarge shi da yunkurin tserewa daga inda ake tsare da shi tsawon watanni kusan uku, inda suka bukaci mahukuntan na Nijar su gaggauta sakin shugaba Bazoum da iyalinsa .
Sojojin da suka yi juyin mulki ranar 26 ga watan Yulin 2023 a Jamhuriyar Nijar sun sanar da dakile wani yunkurin arcewar hambararren Shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa daga inda ake tsare da su.
A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin mata sun yi zaman dirshan a harabar ofishin CEDEAO na birnin Yamai da nufin jan hankalin shugabanin kungiyar da su janye takunkumin da suka sanya wa Nijar sanadiyar juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar kashe gomman ‘yan ta’adda yayinda sojoji 6 suka rasu wasu 18 suka ji rauni sakamakon gumurzun da aka yi a arewacin jihar Tilabery.
A wani yunkurin samar da kudaden daukar dawainiyar al’amuran gudanar da sha’anin mulkin gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar, gwamnatin mulkin soji ta kafa wata gidauniya da nufin tattara gudummawar kudade daga ‘yan kasar na ciki da waje.
A Jamhuriyar Nijar mambobin kungiyar Mata Masu Dubara (MMD) sun yi gangami a harabar babban bankin kasashen Afrika ta yamma rainon Faransa (BCEAO) don matsa lamba wa shugabannin bankin su mayar wa kasar kudaden ajiyarta wadanda takunkumin kungiyar UEMOA ya rutsa da su sakamakon juyin mulki.
Wani alkalin kotun Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar ya bada belin ‘yar jaridar nan Samira Sabou, bayan da ta shafe kwanaki 4 a hannun ‘yan sandan farin kaya.
Rukunin farko na sojojin Faransa sun fice daga Nijar zuwa gida bayan shafe watanni sama da 2 ana kace -nace akan wannan batu da ya haifar da tankiyar diflomasiyya tsakanin sojojin juyin mulkin 26 ga watan Yuli da hukumomin Faransa.
A jamhuriyar Nijer ‘Yar jaridar nan mai fafutuka ta yanar gizo, Samira Sabou da ta yi batan dabo a karshen watan Satumba ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata.
Ko da yake ba'a bayyana dalilan daukan wannan mataki a hukumance ba ‘yan rajin kare hakkin masaya na ganin abin a matsayin wata hanyar samar da wadatar gas ga al’ummar kasar ne.
Kungiyar M62 ta gabatar da takarda a ofishin ministan harkokin wajen Nijar akan bukatar maka tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou a kotun kasa da kasa ta ICC, saboda zarginsa da aikata miyagun laifuka da zama silar aika-aikar ‘yan ta’addan da ake fama da su, abinda makusantansa ke cewa zancen banza ne.
Domin Kari