Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharudan ECOWAS Sun Haifar Da Muhawara A Nijar


Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

A jamhuriyar Nijar ‘yan kasar sun bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da matsayar da shugabannin kasashen kungiyar CEDEAO su ka cimma a karshen taron da suka gudanar a ranar Lahadi, dangane da rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Gaggauta tsara daftarin da zai bai wa gwamnatin rikon kwarya damar gudanar da ayyukanta a wani dan gajeren wa’adi na daga cikin sharudan da aka gindaya wa hukumomin mulkin sojan Nijar, a karshen taron shugabannin ECOWAS na ranar Lahadi, abin da ke nufin a karon farko kungiyar ta aminta da juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli.

Taron shugabannin kungiyar ECOWAS ya bukaci a gaggauta sakin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa da ma dukkan mutanen da aka kama a sakamakon wannan al’amari, kafin a fara duba hanyoyin dage takunkumin da aka kakaba wa kasar.

Shugaban kungiyar farar hula ta MOJEN, Siraji Issa, ya ce "yanzu kwallo ta koma wajen wadannan sojoji, in dai suna tausayawa al’ummar Nijar, sannan kuma suna jin koke-koken al’umma da bala’i da fatara da yau al’ummar Nijar ta shiga ciki, to hakika ba wurin zuwa sai gona."

Issa ya ce ya kamata su amince da wadannan sharudan a take yanke, kuma ya kasance wannan kasa ta koma bisa ga tafarkin dimokaradiyya.

Tsara zabubbuka a yunkurin mayar da al’amuran mulki a hannun fararen hula na daga cikin abubuwan da kungiyar CEDEAO ta umurci hukumomin Nijer a kansu.

To sai dai a nasa ra’ayin wani dan siyasa, Kane Habibou Kadaoure, ya ce yana ganin lokaci bai yi ba, da za'a maida hankali kan wannan batu, domin a cewarsa akwai wasu batutuwan na daban da suka fi cancanta a bai wa fifiko.

Taron ya nada Shugaban kasar Togo Faure Eyadema da Patrice Talon na Benin da shugaban Saliyo Julius Maada Bio, domin su shugabanci kwamitin shiga tsakani don ganin an warware rikicin siyasar ta Nijar.

Kungiyar ta jaddada cewa, za ta ci gaba da saka ido domin tantance halin da ake ciki game da batun mutunta sharudan da ta gindaya, tana mai ikirarin amfani da karfi matsawar ta fahimci sako-sako a shirin mayar da kasar kan tafarkin dimokaradiya.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG