Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kallo Ya Koma Abuja Yayinda Ake Shirin Taron ECOWAS a Ranar 10 Ga Watan Dizamba Na 2023.


ECOWAS
ECOWAS

A yayinda shugabanin kasashen yammacin Afrika membobin kungiyar ECOWAS ke shirin gudanar da taro a gobe Lahadi 10 ga watan Disamba a Abuja domin yin nazari kan mataki na gaba kan sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin fararen hula kasar sun bukaci ECOWAS ta tausaya wa talakka.

Wasu kungiyoyin fararen hular a Nijer kasar sun yi kira ga kungiyar ECOWAS ta tausaya wa talakkawan kasar ta janye takunkumin da ta kakaba mata. Kungiyoyin sun kuma bukaci bangarori su zauna kan teburin sulhu don warware rikicin siyasar ta Nijer cikin ruwan sanyi.

Madame Hadiza Djermakoye wacce ta ari baki ta ciwa wasu kungiyoyin fararen hula a karkashin jagorancin kungiyar DCTR albasa da sako zuwa ga shugabanin CEDEAO dangane da halin da ake ciki a Nijer, sanadiyar takunkuman da kungiyar ta kakaba wa kasar sakamakon juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Kungiyoyin sun ce kimanin watanni 5 bayan barkewar wannan dambarwar, talakkawa na shan gashin aya mayuka, sakamakon tsayawar al’amura a mahimman fannoni da dama.

A gobe Lahadi 10 ga watan Disamba ne shugabanin kasashen yammacin Afrika zasu gana a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja inda ake sa ran za su tattauna don gano hanyoyin da za su bullowa rikicin siyasar na Nijar; lamarin kungiyoyin fararen hula karkashin jagorancin DCTR suka bijiro da abin da suka ayyana shi da shawarwarin samar da hanyar gano bakin zaren wannan kulli. Kuma a cewarsu, ta haka ne talakka zai fita daga kangin rayuwar da ya tsinci kansa ciki.

Kazalika, wasu kungiyoyin na daban sun yi dafifi daga dandalin place Toumo zuwa dandalin Place de la Resistance inda suka kafa zaman dirshan har zuwa karshen taron CEDEAO a matsayin wani matakin tursasa wa kungiyar ta janye takunkuman da ta kakaba wa Nijar ko kuma kasar ta fice don maida hankali kacokam kan kungiyar kasashe 3 na sahel AES.

A saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

KIRAN DAGE TAKUNKUMI.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG