Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun UEMOA Ta Dora Alhakin Halin Matsin Da Ake Ciki A Nijar A Wuyar Sojojin Da Su Ka Yi Juyin Mulki


UEMOA
UEMOA

Hukumomin Mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadi game da hukuncin  kotun  kasashen yammacin Afrika rainon Faransa UEMOA ta yanke dangane da bukatar janye takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar din da na ECOWAS a washe garin juyin Mulkin 26 ga watan Yuli.

Kotun ta dora alhakin halin matsin da aka shiga a kasar a wuyar sojojin da suka kifar da zababben shugaban kasa, Mohamed Bazoum, saboda haka mayar da shi kan kujerarsa ita ce mafitar wannan al’amari, a cewar alkalin kotun.

Hukuncin da gwamnatin rikon kwaryar Nijar ke ganinsa tamkar mai nasaba da dalilan siyasa.

Kungiyar UEMOA, wace ta kunshi kasashe 8 na yammacin Afrika masu amfani da kudaden CFA, ta bi sahu a zaman da ta gudanar a Abuja, daura da taron kungiyar CEDEAO na ranar 30 ga Watan Yuli. Saboda haka kungiyar mai kula da harakokin kasuwanci, sha'anin kudi da zirga-zirga, ta yanke shawarar yi wa Nijar kamuwar kudade da kadarorinta da ke ajiye a bankin bankuna na BCEAO, mai cibiya a Dakar babban birnin Sénégal.

Matakin da hukumomin mulkin sojan Nijar da wasu kungiyoyi 7 suka kalubalanta a kotun UEMOA da ke Ouagadougou a bisa bukatar ta jingine shi zuwa lokacin kammala shari'ar da ke tsakanin sabin hukumomin da shugabanin kasashen Afrika ta yamma.

A hukuncin ta yanke a karshen makon jiya kotun ta dora alhakin abubuwan da suka wakana a wuyan sojojin da suka hambarar da zabeben shugaban kasa, kamar yadda ministan shari’ar Nijar mai shari’a Alio Daouda ya bayyana wa taron manema labarai. Ya ce ba su da ko labarin ranar shara'an, sai dai kawai su ka ji kwasam cewa an yi shari'a kuma an ba su rashin gaskiya.

Bayan nazarin wannan shari’a, mahukuntan Nijar na ganin alamun an fake da dalilan siyasa wajen yanke hukunci inji ministan shari’a.

A wata ranar ta gaba da kawo yanzu ba a bayyana ba ne kotun ta UEMOA za ta saurari bangarori a yayin zaman da aka kira na zurfafa bincike a shari’ar da ke tsakanin hadin gwiwar hukumomin mulkin sojan Nijar da wasu kungiyoyi 7, da a dai gefe shugabanin kungiyar kasashen yammacin Afrika masu amfani da kudaden CFA.

Saurari rahoton Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG