Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Bikin Cika Shekara 65 Da Zama Jamhuriya


Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, yayin da yake bayani ta gidan talabijin a ranar 28 ga watan Yuli.
Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, yayin da yake bayani ta gidan talabijin a ranar 28 ga watan Yuli.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya jinjina wa al’ummar wannan kasa, saboda yadda suka jure wa matsalolin da suka biyo bayan takunkumin kungiyar CEDEAO da UEMOA.

A yayin da a ranar Litinin 18 ga watan Disamba kasar Nijar ke bukukuwan cika shekaru 65 da zama jamhuriya, shugaban gwamnatin mulkin sojan CNSP, Janar Abdourahaman Tchiani, ya yi jawabi ta kafafen yada labaran gwamnati a ranar jajiberi, domin bitar halin da ake ciki a kasar a tsawon wadanan gwamman shekaru.

Ya na mai jaddada alwashin samar da mafitar dambarwar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Batun tsaro na daga cikin muhimman batutuwan da shugaban majalisar CNSP ya tabo a wannan jawabi na ranar jamhuriya da ke zuwa a wani lokacin da Nijar ta yanke hulda a fannin tsaro da tsohuwar kasar mulkin mallaka Faransa, inda ya ce tuni aka fara ganin haske a fagen daga.

Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce a dalilin nasarorin da dakarun tsaronmu ke samu, al’amuran tsaro sun fara daidaituwa sannu a hankali, ya ce abu na zahiri shi ne yadda wasu ‘yan gudun hijirar cikin gida suka fara koma garuruwansu, haka kuma makarantu kusan 200 sun sake budewa a jihar Tilaberi, bayan da suka kasance rufe a tsawon shekaru kusan 2 sanadiyar matsalolin tsaro, sannan mun dauki matakan samar da tsaro kan hanyar shigo da kayan abinci da magunguna da kuma yadda harakokin yau da kullum suka fara dawowa a yankuna da dama.

A cewarsa, kafuwar kungiyar AES mataki ne na ci gaban kudirin mayar da Sahel wani yankin zaman lafiya da jin dadin rayuwa.

A fannin yaki da cin hanci, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce hukumar COLDEFF na nan kan aiki domin bude bincike kan badakalolin da take da hurumi akan su. Ya na mai jaddada goyon baya ga mambobin wannan hukuma su yi aiki dangance da rantsuwar da suka yi ta yadda al’umma za ta ba su yarda.

Ya kara nanata alkawalinsa da na takwarorinsa na CNSP da gwamnati cewa, ba za su taba bai wa kowa kariya ba. Sanannen abu ne kamarin da cin hanci ya yi a wannan kasa na daga cikin manyan dalilan da ya sa suka hambarar da gwamnati, in ji shi.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya jinjina wa al’ummar wannan kasa, saboda yadda suka jure wa matsalolin da suka biyo bayan takunkumin kungiyar CEDEAO da UEMOA, ya ci gaba da cewa ‘yan Nijar sun gwada kishin kasa.

Ya kuma yi amfani da wannan dama don mayar da martani ga wadannan kungiyoyi dangane da sharudan da suka gindaya a baya bayan nan.

Ya ce ba za mu taba amincewa dukkan wani jan rai ba, ba kuma za a kara tsoratar da mu ba ko a shimfida mana wata ka’ida ba. kanmu hade yake domin ceton kasa.

Janar Abdouraamane Tchiani ya sha alwashin yin abubuwan da ke yiwuwa, domin tabbatar da ci gaba samar da tsaro da ayyukan jin dadin rayuwar jama’a da hada kan ‘yan kasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG