A ci gaba da laluben hanyoyin warware kiki kakar da ke tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da shugabanin kungiyar CEDEAO mataimakiyar sakataren Harkokin Wajen Amurka din mai kula da harakokin Afrika Molly Phee ta yi rangadi a Nijar inda ta gana da Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine da mukarrabansa a wannan Laraba.
La’akari da koma bayan da kace nacen da ya biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 ya haifar wa al’ummar Nijer a harakokin yau da kullum ya sa Amurka ta dage da yunkurin sasanta bangarorin da ke wannan takaddama mafari kenan bayan ta halarci taron kasashen CEDEAO a matsayin ‘yar kallo Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afrika Molly Phee ta sauka a birnin Yamai inda suka tattauna da hukumomin rikon kwaryar kasar a wannan laraba 13 ga watan Disamba, kamar yadda ta bayyana a taron manema labarai.
Ta ce na bayyana masu matsayin Amurka da ke nufin mun fi son a yi cudanya a maimakon rarrabuwar kai a tsakanin Nijer da makwabtanta. Na kuma jaddada kwarin gwiwa ga CNSP ta yi na’am da shawarwarin kungiyar ECOWAS domin karfafa hanyoyin sulhu.
Amurka na goyon bayan matsayar da ECOWAS ta cimma musamman batutuwa kamar haka.
Ya kamata CNSP ta bayar da wa’adin da za a gudanar da al’amuran mulkin rikon kwarya wanda zai kasance a gajeren lokaci domin mayar da al’amura a hannun wata zababbiyar gwamnatin farar hula. Muna kuma goyon bayan kungiyar ECOWAS a kudirinta na dage takunkumi sannu a hankali a matsayin amsa ga kokarin da CNSP za ta yi a nan gaba.
Makomar hambararren shugaban kasa da mukarraban gwamnatinsa na daga cikin batutuwan da ambasada Molly Phee ta tattauna a kansu da Firaminista Zeine tare da halartar ministansa na cikin gida da na tsaro da na harkokin waje.
Ta ce mun kuma tsayar da maganar da muke ganin ta na da mahimmancin sosai; ma’ana cimma daidaito kan makomar tsohon shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa da mambobin gwamnatinsa. A tattaunawarmu na jaddada masu matsayin Amurka game da shirin farfado da huldar da ta ta'allaka akan harkokin tsaro da ayyukan ci gaban al’umma dangance da yadda kokarin CNSP zai kasance a gaba.
Alkawalin da Amurka ta dauka a nan Yamai da Abuja da sauran kasashen CEDEAO shine karfafa wa al’ummar Nijer guiwa donganin hakarsu ta cimma a kokarinsu na shimdida dimokradiya cikin yanayin kwanciyar hankali.
Da ta ke amsa tambaya kan kwankwasa kofar da Rasha ta fara yi a Nijer bayan juyin mulkin 26 ga watan yuli Molly Phee ta bayyana cewa dadaddiyar hulda ce ke tsakanin Amurka da Nijer kuma sanannen abu ne cewa an sami kyakkyawan sakamako a yaki da ta’addancin da muka sa gaba. Na gaya wa CNSP gaskiya kan cewa za mu ci gaba da aiki amma kuma mu kasance masu mutunta manufofin kasashenmu 2.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna