Matakin wanda ke shafar firsinonin da kotu ta riga ta yanke wa hukunci a baya, abu ne da ke takaita tsawon wa’adin zaman wakafi ga wani rukunin ‘yan kaso, yayin da ta wani bangare, abin ke bai wa wasu damar fita daga kurkuku kwata kwata.
Yanayin lafiya na daga cikin manyan dalilan da ake amfani da su wajen tantance ‘yan kason da ya kamata su ci moriyar wannan tsari.
Sassauta hukuncin kisa zuwa zaman kason rai da rai, kamar yadda yake rubuce a takardar afuwar da Shugaban majalissar CNSP, Janar Tchiani ya saka wa hannu abu ne da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke kallo da mahimmanci inji AbdelNasser Na Hantsi na Makarantar Dimokradiya.
Hakazalika, wani jigo a reshen Nijar na gamayyar Kungiyoyin Yaki da Hukuncin Kisa, Alhaji Moustapha Kadi, wadda ya yaba wa matakin na ganinsa tamkar wata hanyar rage cunkoson jama’a a gidajen yari.
Koda yake ba a bayyana yawan wadanda matakin ya shafa ba, wasu ‘yan kasar sun fi so su gani an maida hankali wajen halin da firsinonin siyasa irin su hambararren Shugaban Kasa, Mohamed Bazoum, ke ciki.
Kasancewar matakin na zuwa a wani lokacin da dimbin ‘yan siyasa ke kule a gidajen yari daban daban tun washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023, ya sa Shugaban Kungiyar Farar Hula ta FCR, Souley Oumarou ankararda hukumomin mulkin soja, su dubi halin da wadanan mutane ke ciki da idon rahama.
To sai dai fa matakin afuwar bai shafi mutanen da aka kama da aikata manyan laifuka ba irinsu amfani da takardun bogi, cin hanci, halitta kudaden haram, kera kudaden jabu, handamar dukiyar kasa, fataucin myagun kwayoyi, ta’addanci da yi wa kasa zagon kasa da bautar da dan adam da dai sauransu.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma, ya aiko mana da karin bayani.
Dandalin Mu Tattauna