Kasashen biyu da ke takun saka da kasar da ta yi masu mulkin mallaka sun ce sun gano cewa suna tafka asarar makuddan kudaden haraji a dalilin wannan yarjejeniya.
Lura da abinda aka kira take taken da Faransa ta sa gaba a yunkurin haddasa tarnaki wa kasar Nijar da kasar Mali ya sa gwamnatocin rikon kwaryar kasashen biyu yanke shawarar dakatar da sassaucin harajin da suka shafe gomman shekaru su na yi wa kasar ta Faransa a karkashin yarjejeniyar da ke cewa kamfanonin da ke zaune a wadanan kasashe ba za su biya ko tamma ba na haraji. Abin da babban magatakardan kungiyar Ma’aikatan Haraji ta SNAI, Moussa Oumarou ya ce ya yi daidai.
Matakin wanda zai fara aiki a nan gaba bayan watanni 3 abu ne da ake ganin zai taimaka sosai wajen samar da kudaden shiga a aljihun gwamnatin kowacce daga cikin wadannan kasashe.
Da ma dai tun a ranakun farkon takaddamar da ta taso a tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da hukumomin Faransa a nan cikin gida wasu daga cikin ‘yan kasuwa kamar su Jamilou ibrahim suka shiga yunkurin ankarar da mahukunta cewa lokaci ya yi da za a soma tatsar kudaden haraji daga kamfanonin Faransa.
Sanarwar gwamnatin rikon kwaryar Nijar da ta Mali ta jaddada cewa kasashen 2 sun jinginu da sharuddan da ke kunshe a yarjejeniyar birnin Vienna ta 1969 wace ke cewa tsarin huldar kasashe abu ne da ya yi tanadin cewa kowace kasa na da cikakken ‘yancin daukar matsayin da ya dace dangance da abin da ta ke ganin shi ne mafi a’ala wajen kare muradunta da na al’ummarta.
Kawo yanzu ba wani martani daga gwamnatin Faransa akan wannan sabon mataki.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna