Da ya ke bayani a wata hira da aka watsa ta kafar talabijin mallakar gwamnati jim kadan bayan kammala taron shugabannin kasashen yammacin Afrika (CEDEAO), Janar Abdourahamane Tchiani ya tabo batun tsare hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum da iyalinsa, inda ya ce ba a gidan kaso su ke tsare ba, suna cikin gidansa, kuma sun ba iyalinsa damar tafiya duk inda su ke so amma Bazoum ya ki, ya na mai cewa in dai ba tare da iyalinsa zai tafi ba, gwamma su zauna.
Shugaban majalisar CNSP na ganin sakin shugaba Bazoum a halin da ake ciki a yau a Nijar wani abu ne da ka iya zama babbar barazana.
Dangane da batun takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa kasar da kuma irin sharudan da ta gindaya, shugaban gwamnatin mulkin sojan na ganin akwai wata manufar boye tattare da wannan lamari.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna