Kujerar Ciyaman din APC a jihar Neja ta fara rawa, a kalla, biyo bayan rawar da ake zargin ya taka a faduwa zabe da wasu 'yan takarar jam'iyyar su ka yi.
Yayin da hukumomi a matakai daban-daban na Najeriya ke ci gaba da janyo hankalin ‘yan kasar akan muhimmancin ‘yin babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali da zaman Lafiya, ba haka take ba a garin Salka dake Jihar Neja.
Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci ‘yan Nigeria da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun shugabanni na gari masu tausayin al’umma a babban zaben kasar dake tafe a cikin wannan wata.
Gwamnatin jihar Neja da ke Najeriya ta bayar da umarnin bindige duk wani dan sara-suka da ya nemi tayar da hankalin jama’a a birnin Minna.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Nejan Najeriya ta ce ta gano wani sabon shiri na yin magudi a lokacin gudanar da babban zaben kasar da ke karatowa.
Bayan kubutar da yan kasar China 7 da yan bindiga suka sace a jihar Neja, 'yan bindiga sun kashe wasu mutane 7 ta hanyar banka masu wuta a rami a jihar Neja.
Bayanai dai sun tabbatar da cewa akwai daruruwan mutanen da suka bar garuruwansu saboda tashin hankalin ‘yan fashin daji masu satar mutane domin neman kudin fansa da wani lokaci ma suke halaka jama’a.
Bayanai dai na kara fitowa game da mummunar arangamar da jami’an tsaron sojin Najeriya suka yi da mayakan kungiyar Boko-Haram a yankin karamar hukumar Borgu ta Jihar Nejan Najeriya.
Daruruwan 'yan kasar Jamhuriyar Nijar da ke zaune a Najeriya na ci gaba da yin tururuwa zuwa yin rujistar zabe da hukumar zaben kasar ta Nijar wato SENI ke yi.
Daruruwan 'yan kasar Janhuriyar Nijar dake zaune a Nigeria na ci gaba da yin tururuwa zuwa yin rujistar zabe da hukumar zaben kasar ta Nijar wato SENI ke gudanarwa.
A yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Neja ta Najeria na can na kokarin shawon wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Salka na karamar hukumar Magama a Jihar Nejan.
Gwamnatin jihar Neja da ke Najeriya na ci gaba da kokarin sake tsugunnar da al’ummomin garin Kpata Kacha da ke yankin karamar hukumar Mokwa da suka tarwatse a sakamakon wani rikicin mallakar fili tun a shekara ta 2018.
Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka akwai daruruwan makarantun firamare da sakandire da ke rufe a sakamakon matsalar ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa.
A yayin da Najeriya ke cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga turawan kasar Birtaniya da suka yi wa kasar mulkin mallaka, tsofaffin shugabannin mulkin soja a kasar sun bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa a dunkule.
Har yanzu dai ‘yan fashin daji na ci gaba da kai hare-hare da kisan jama’a a wasu yankuna na Jihar Nejan Najeriya, wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin kakar debe amfanin gona ke kawo jiki.
A ranar Juma'a 23 ga watan Satumba ne hukumar kula da wuraren da ke da tashoshin samar da hasken lantarki a Najeriya ta HYPPADEC ta fara rabon kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta yiwa barna a jihohi 6 da ke karkashin wannan hukuma.
Kwamitin wanzar da zaman lafiya a tsakanin ‘yan Najeriya da tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar, ke shugabanta ya gudanar da wani taro a Minna, fadar Gwamnatin Jihar Neja.
Jam’iyyar APC Mai Mulki a Najeiriya na gudanar da tarurruka daban daban da nufin kara dinke duk wata barakar dake tsakanin yayanta kafin babban zaben na badi.
Ganawar dai na zuwa ne a daidai Lokacin da babban zaben shekara ta 2023 ke kara gabatowa a Nigeriar, ko da yake dai tsofaffin shugabannin, Janar Babangida da Janar Abdussalam ba su ce wa manema labarai komai ba akan wannan ganawar.
Majalisar Dokokin jIhar Nejan Nigeria ta bayar da Sanarwar Dakatar da zababbun shugabannin kananan Hukumomi 15 dag cikin 25 dake fadin jihar Nejan da ake kan bincikensu.
Domin Kari