NIGER, NIGERIA - A Jihar Neja kimanin ‘yan kasar Nijar 5000 ne ake sa ran za su yi rijistar zaben da zata basu damar kada kuri’a a Najeriya a lokacin gudanar da zaben a can kasar Nijar.
Sai dai ‘yan Nijar din da muka samu suna bin layin rijistar a birnin Minna sun ce lokacin da aka dibar masu ya yi kadan, kamar yadda shi ma shugaban kungiyar ‘yan kasar ta Nijar mazauna Jihar Neja, Alhaji Dalladi Ali, ya ce.
Babban jami'in hukumar zaben ta kasar Nijar dake aikin rijistar a jihar Neja Abdu Amadu Ibrahim ya ce lokacin da aka dibar masu zai ishesu su kammala aikin rijistar.
Bayanai dai sun nuna cewa idan ba a samu mutane 2000 ba a wannan rijista to ‘yan Nijar dake Jihar Neja za su tafi Abuja ne domin kada kuri’a a lokacin da za a gudanar da zaben.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari: