Bayan kammala Zaben Shugaban kasa da na yan majalisar kasa a Nigeria, yanzu haka wata mummunar baraka ta kunno kai a cikin jam,iyyar APC a Jihar Neja dake Arewa maso tsakiyar kasar,
APC dai ita ce ta samu kuri,u mafi rinjaye a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Fabrairu a jihar Neja, amma ta rasa kujerar Sanata guda sannan ta rasa kujerun Majalisar Wakilai guda 3 a ciki har da na Chanchanga, fadar Gwamnatin jihar Nejan,
A yanzu dai APC ta sanar da dakatar da Shugabanta na jihar Nejan Hon.Halliru Zakari Jikantora daga zama Mamba na APC a matakin gundumar Kashani ta yankin Karamar Hukumar Agwara wato gundumar da shi Shugaban APC na jihar Nejan ya fito,
A wani taron manema Labarai a Minna, Shugaban APC a gundumar Kashani, Abdullahi Amadu, ya gode ya ce sun dauki wannan mataki ne saboda zagon kasa da suka ce yana yi ma APC kamar yadda yayi Karin Bayani
Shi ma sakataren Jam'iyyar APC a yankin karamar hukumar ta Agwara Shu'aibu Usman Gado ya ce suna da laifuffukan da ake zargin shi shugaban APC na jihar Nejan ya aikata.
To amma shugaban APC na Jihar Nejan, Hon. Halliru jikantoro, ya yi watsi da wannan mataki sannan ya musanta zargin da ake yi ma shi.
Wannan dambarwa dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin komawa runfunan zabe domin kada kuri'un zaben Gwamnoni da na yan majalisar jihohi.
Saurari cikakken rahoton: