Wannan rikicin dai ya barke ne a tsakanin mutanen Kacha da ke hedikwatar karamar hukumar Kacha a wancan lokaci, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayukka da kona daruruwan gidaje dama dukiya mai dimbin yawa, da yasa har ya zuwa wannan lokaci mutane garin Kpata Kacha ke tarwatse a wasu garuruwa na daban.
Garin na Kpata Kacha dai ya yi suna sosai wajan hada-hadar kasuwancin kifi, kasancewarsa a bakin Kogi Kwara, sannan ya shahara wajan kasuwancin katako da kuma noman, baya ga hanyar jirgin kasa da ta ratsa ta garin.
A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, gwamnati jihar Neja ta share tsawon wuni tana tattaunawa da Shugabannin bangarorin guda biyu da nufin sasantasu.
Sakataren gwamnatin jihar , Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, da ya jagoranci zaman ya ce “zaman ya kusa kai wa karshe kuma abubuwan da aka tattauna dama abubuwa ne wadanda kowa yana da na shi na akidar da ya rike.”
Matane ya ce “ Abinda mutanen Kacha suke so shi ne mutanen Kpata Kacha su yi mubayi’a su kawo kan su cewa suna karkashin shi Na Kacha din kuma wannan ba’a samu matsala ba kowa ya yadda da wannan.”
Sakataren Sarkin Kacha da ake kira Sheshi Kacha, Alhaji Tijjani Ndaliman Kacha, ya ce sun gamsu da zaman da aka yi tsakanin Kacha da Kpata Kacha, mu uwa daya uba daya ne, kuma Allah ya kawo wannan matsalar. Ya ce gwamnati ta damu kwarai suma sun damu kwarai, ba wanda zai so ya ga dan' uwansa yana shan wuya, an kirasu a sasanta su kuma za su je su maida sako a gida a cikin sati biyu za su zo su gaya musu yadda suka yi.”
Tsohon Shugaban majalisar dokokin jihar Neja Hon. Ndanusa Hassan, shine ya wakilci mutanen Kpata kacha a wannan zama na ranar Alhamis, ya ce sun yarda da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka shimfida.
A yanzu dai bayan makonni biyu nan gaba ne ake sa ran za’a kai karshen wannan zama na zullumi a tsakanin wadannan bangarori guda biyu da tarihi ya nuna cewa sun share sama da shekaru 200 suna zaman tare a cikin aminci da juna.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari: