Washington, DC —
Wannan Al'amari dai yasa mazauna wasu yankunan karkara inda lamarin yafi kamari kara shiga cikin wani yanayi na tashin hankali.
Wakilin Muryar Anurka a jihar Nija ya tattauna da wani Mazaunin Garin Kuimo ta karamar Hukumar Mariga a jihar ta Nija, wanda yace tun a karshen makon da ya gabata suke cikin yanayi na tashin hankali domin kuwa ko a lokacin da suke magana da shi suna kan tsauni sakamakon musayar wuta da a ke yi a tsakanin 'yan bindigar da sojojin.
A garin Adunu ma na karamar Hukumar Paikoro Al'ummar garin na cikin tashin hankali bayan samun labarin cewa, 'yan bindigar sun hallaka mutane 6 daga mutanen garin su kimanin 50 da suka yi garkuwa da su a makon jiya a cewar Alhaji Bakana, Sarkin Hausawam garin na Adunu.
Kawo lokacin hada wannan rahoto dai kokarin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar Nejan yaci tura. Haka zalika Gwamnatin jihar Nejan batayi wani karin Haske ba akan lamarin.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: