Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Harbe Duk Wani Dan Sara-Suka Da Ya Dauki Makami a Minna – Gwamnatin Neja


Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Gwamnatin jihar Neja da ke Najeriya ta bayar da umarnin bindige duk wani dan sara-suka da ya nemi tayar da hankalin jama’a a birnin Minna.

Matsalar yan sara suka na ci gaba da zama wata babbar barazana ga al’ummar da ke zaune a Minna babban birnin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Rohotanni dai sun nuna yadda matsalar ‘yan sara sukar, wadanda akasarin su matasa ne ke aukawa jama’a tare da wawushe shaguna da kisan jama’a babu gaira babu dalili.

Sakataren gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya ce gwamnatin ta dauki wannan mataki ne saboda abun yaki ci yaki cinyewa, kusan duk kwana biyu ‘yan ta’addan suna fitowa suna addabar mutane,

Ya ce a wasu wuraren ma ana kashe mutum daya, biyu zuwa uku, shi ya sa gwamnati ta ba jami’an tsaro umarnin duk matakan da ya kamata su dauka domin su kawo karshen wannan su dauka.

Makamai
Makamai

Tuni dai mazauna birnin Minna suka fara nuna farin cikinsu da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka, domin kawo karshen wannan matsalar da kowa ke kokawa.

A yanzu dai lokaci ne zai nuna tasirin wannan mataki, a daidai lokacin da wasu kananan hukumomin jihar Neja ke fama da matsalar ‘yan fashin daji, al’amarin da ke kara jefa fargaba ga jama’a a daidai lokacin da babban zaben Najeriyar yake kawo jiki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

XS
SM
MD
LG